Xi Jinping ya ce, ana fuskantar sauye sauye a nan duniya, amma kawo yanzu, ba a canja babban burin neman ci gaba cikin zaman lafiya ba, a sa'i daya kuma, mutanen duniya suna fuskantar kulubaloli da dama. Kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da kasa da kasa domin kafa dangantakar dake tsakanin kasashen duniya bisa ka'idojin girmama juna, nuna adalci, da yin hadin gwiwa da kuma cin moriyar juna, ta yadda za a kara dunkulewar dukkanin bil Adam, da kuma ba da gudummawa yadda ya kamata wajen kiyaye zaman lafiya da neman bunkasuwar kasa da kasa. (Maryam)