Alkaluman dake kunshe cikin rahoton sun nuna karuwar da sashen cinikayyar wajen kasar ya samu a cikin watanni tara na farkon shekarar. Kaza lika bisa alkaluman hukumar kwastam, kayayyakin da Sin ta yi cinikayyar su sun karu da kaso 11.1 bisa dari a shekarar, wadanda kudin su ya kai kimanin dalar Amurka kusan triliyan 4 a watanni 11 na farkon shekarar.
To sai dai kuma a cewar rahoton, sashen na iya fuskantar koma baya idan aka kwatanta da ci gaban da ya samu a shekarar bara. Har ila yau rahoton ya nuna irin tagomashi da tattalin arzikin Sin ke nunawa, inda alamu ke nuna dagawar matsayin sa daga matsakaici zuwa mafi girman matsayi, wanda hakan ke alamanta kafuwar wani ginshiki na fadadar ci gaban cinikayyar kasashen waje ta Sin.