in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta bukaci gudanar da zaben DRC cikin kyakkyawan yanayi
2018-12-17 10:29:48 cri
Shugaban hukumar zartaswar tarayyar Afirka ta AU Moussa Faki Mahamat, ya shawarci 'yan siyasa, da masu ruwa da tsaki a babban zaben jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, da su nuna sanin ya kamata, yayin babban zaben kasar na ranar 23 ga watan nan.

Moussa Faki Mahamat, wanda ya bayyana damuwa game da asarar rayuka da aka samu a wasu yankunan kasar a lokutan yakin neman zaben, ya ce hakan na iya yin barazana ga nasarar zaben dake tafe. Don haka a cewar sa, ya kamata 'yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki, su rungumi akidar siyasa, su kuma tabbatar da gudanar zaben cikin lumana da adalci, kamar yadda dokokin zabe na kasashen Afirka, da ma na sauran kasashen duniya suka tanada.

Ya kuma nuna damuwa, game da konewar kayan zabe a birnin Kinshasa, sakamakon wata gobara da ta tashi a wani rumbun adana kayayyaki na hukumar zaben kasar, tsakanin ranekun 12 zuwa 13 ga watan nan.

Wata sanarwa da kungiyar AU ta fitar a jiya Lahadi, ta ce an samu asarar rayuka a yankunan Kalemie, da Lubumbashi da Mbuji-Mayi, yayin da ake daf da gudanar da babban zaben kasar na karshen mako.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China