in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Ghana ya kori alkalai uku daga aiki
2018-12-17 10:41:25 cri
Shugaba Nana Akufo-Addo na kasar Ghana, ya kori alkalan manyan kotunan kasar sa uku daga bakin aiki, sakamakon aikata laifuka masu nasaba da cin hanci da rashawa.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar a jiya Lahadi, ta ce an kori mai shari'a Ayisi Addo, da Uuter Paul Dery, da Mustapha Logoh daga aikin su ne, sakamakon shawarar kwamitin binciken zargin da aka yi musu. Kwamitin ya hakkake cewa, halayyar da alkalan suka nuna, ta sabawa dokokin kasar Ghana.

Babbar mai shari'a ta kasar Sophia Akuffo ce dai ta kafa kwamitin binciken, bayan da dan jaridar nan mai kwarmata bayanai Anas Aremeyaw Anas ya gabatar da korafi a kan su.

Alkalan uku dai na cikin jimillar alkalai 22, na manya da kananan kotunan kasar da aka zarga da aikata cin hanci da rashawa shekaru uku da suka gaba.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China