Jami'in ya bayyana hakan ne yayin taron masu ruwa da tsaki, game da cikar kasar Sin shekaru 40 da fara aiwatar da manufofin gyare gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje.
Ya ce Sin ta gudanar da manyan ayyuka da suka shafi nazari, da binciken kwayoyin halittar tsirrai, ta kuma tattara muhimman bayanan kimiyya game da wasu nau'o'in hatsi, kamar shinkafa, da alkama da masara da ake nomawa a kasar. Kaza lika an gudanar da irin wannan aiki a fannin dabbobin kiwo kamar shanu da tumaki.
Zhang Hecheng ya kara da cewa, Sin ta cimma nasarori a ayyukan tagwaita irin shinkafa, da yaki da cututtukan dake addabar dabbobi da wasu tsirrai. Daga nan sai ya yi kira ga daukacin masu ruwa da tsaki a fannin raya noma a kasar, da su kara azama wajen fadada kirkire kirkire, da samar da ci gaba a ayyukan noma na zamani.