A ranar Alhamis majalisar dattijan Amurka ta kada kuri'ar neman a kawo karshen tallafin sojin da Amurka ke bayarwa ga dakarun hadin gwiwa dake yaki a Yemen wanda Saudiyya ke jagoranta, inda majalisar ta zargi yariman Saudi Mohammed bin Salman da hannu wajen mutuwar dan jaridar kasar Khashoggi.
Zargin da majalisar dattijan ta Amurka ke yi, "zargi ne marar kwararan hujjoji, kana zargi ne mai cike da yin shisshigi game da harkokin cikin gidan masarautar Saudiyya, da kuma neman zubarwa masarautar kima a idanun shiyyar da ma duniya bisa ga irin rawar da kasar ke takawa a matakin kasa da kasa," ma'aikatar harkokin wajen Saudi ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa. (Ahmad)