in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cika shekara daya da fara zirga-zirgar jirgin kasa tsakanin Habasha da Djibouti
2019-01-23 08:31:13 cri


A kwanakin baya ne, wato ranar 1 ga watan Janairun shekara ta 2019, rana ce ta cika shekara daya da fara zirga-zirgar layin dogon da ya hada birnin Addis Ababa na kasar Habasha da birnin Djibouti na kasar Djibouti dake gabashin Afirka, wato Addis Ababa Djibouti Railway a turance. Wasu kamfanonin kasar Sin guda biyu sun taimaka wajen gina layin dogon. Wadanne irin sauye-sauye ne layin dogon ya kawo ga zaman rayuwar al'ummar kasashen? Kuma mene ne makomar layin dogon?

Da misalin karfe 8 na safiyar ranar 1 ga watan Janairun shekara ta 2019, a Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha, fasinjoji na shiga cikin jirgin kasa a tasha ta farko ta layin dogo tsakanin Habasha da Djibouti wato tashar Labu. Wadannan fasinjojin ba za su damu da gajiyar doguwar tafiya cikin mota ba, kuma suna jin dadin zirga-zirga ta jirgin kasa daga Habasha zuwa Djibouti, wanda ya fara aikin jigilar fasinjoji a ranar 1 ga watan Janairun shekara ta 2018.

Tsawon layin dogo tsakanin Habasha da Djibouti ya kai kilomita 752.7, wanda kuma saurin tafiyarsa zai iya kaiwa kilomita 120 a awa daya. Kamfanin CCECC, gami da kamfanin CREC na kasar Sin su ne suka yi aikin shimfida layin dogon, wanda ya hada fadar mulkin kasashen biyu wato birnin Addis Ababa da birnin Djibouti. Layin dogon ya kuma zama irinsa na farko na zamani mai aiki da wutar lantarki da aka shimfida a nahiyar Afirka, wanda ya rage yawan lokutan da ake shafewa wajen zirga-zirga a kasa tsakanin Habasha da Djibouti daga mako daya na da, zuwa awoyi goma da 'yan kai a halin yanzu. Har wa yau kuma, saboda tsadar tikitin jirgin sama da wahalar tafiya cikin mota, fasinjoji sun fi zabar jirgin kasa don yin zirga-zirga. Bisa alkaluman da aka yi, zuwa karshen shekara ta 2018, adadin yawan fasinjojin da aka yi jigilarsu ta layin dogo tsakanin Habasha da Djibouti ya tasam ma dubu 130, al'amarin da ya saukakawa mazauna wurin yin zirga-zirga.

Adamu na daya daga cikin fasinjoji wadanda suka yi tafiye-tafiye na yau da kullum ta jirgin kasan, inda ya bayyana cewa:

"Layin dogon shi ne irinsa na farko na zamani mai aiki da wutar lantarki da aka shimfida a nahiyar Afirka, abun dake da babbar ma'ana ga kasar Habasha, da ma nahiyar Afirka baki daya. Layin dogon ba ya taimakawa wajen rage matsin lambar da Habasha take fuskanta ta fannin sufuri kawai ba, har ma ya samar da babban alfanu ga 'ya'yanmu."

Baya ga samar da sauki ga zirga-zirgar fasinjojin, layin dogon shi ma na jigilar kayayyaki da hajoji tsakanin kasashen biyu. Wani jami'in kula da harkokin kasuwanni na kamfanin kiyayewa gami da kula da layin dogo tsakanin Habasha da Djibouti, wato CCECC-CREC JV Project Office a turance, Li Shuangchong ya bayyana cewa, kafin kaddamar da shi a hukumance, tun a shekara ta 2016, bisa bukatar gwamnatin kasar Habasha, layin dogon ya fara aikin jigilar abincin gaggawa don tallafawa mutanen da bala'in fari ya shafa, sa'annan bayan da aka kaddamar da shi, layin dogon ya soma jigilar takin zamani, matakin da ya taimaka ga bunkasa ayyukan noma a kasar. Mista Li ya ce:

"Habasha kasa ce dake da yawan mutane, amma ba ta iya biyan bukatunta ta fannin abinci, har ma tana fuskantar babban matsin lamba wajen jigilar kayayyaki. Layin dogo mai saurin tafiya da muka gina musu, zai iya taimakawa gwamnatin Habasha wajen magance matsalar abinci. Har wa yau kuma, ayyukan gonan kasar na dogaro kan yanayi sosai, alal misali, dole ne a saka takin zamani a wani lokaci na musamman, shi ya sa ayyukan gona za su fuskanci babban matsin lamba a lokacin. Idan hakan ya faru, gwamnatin kasar za ta bukace mu, mu taimaka wajen yin jigilar takin zamani, kuma mun riga mun yi jigilarsa har ton 28483.95."

Habasha kasa ce ta biyu mafiya yawan al'umma a nahiyar Afirka, wadanda ke da babbar bukata ga kayayyaki iri daban-daban, kana rashin iya jigilar kayayyaki na haifar da tsaiko ga ci gaban tattalin arzikin kasar. Ita ma kasar Djibouti tana fatan raya tattalin arzikinta ta hanyar karfafa hadin-gwiwa tare da Habasha, kuma layin dogon ya zama tamkar wata gada tsakaninsu dake kawowa kasashen biyu moriya tare. Tun bayan da aka kaddamar da shi, ya zuwa yanzu, adadin yawan sundukan da aka yi jigilarsu ta layin dogon ya kai 44580, inda yankunan masana'antu dake yankin layin dogon suke kara bunkasa cikin sauri.

A nasa bangaren, babban manajan kamfanin CCECC reshen kasar Habasha Mista Li Zhiyuan ya nuna cewa, shimfida layin dogo tsakanin Habasha da Djibouti, ya taimaka sosai ga ci gaban tattalin arzikin kasashen biyu, inda ya ce:

"A fannin tattalin arziki, a hakikanin gaskiya, layin dogon da aka gina ya taimaka ga raya tattalin arzikin wurin. A halin yanzu a wuraren da layin dogon ya ratsa, ana kokarin gina yankunan masana'antu kimanin goma, wadanda rabinsu aka riga aka fara aiki a ciki. Bayan da aka kaddamar da layin dogo tsakanin Habasha da Djibouti, ya fara taka rawa ta fannin raya masana'antu da sana'o'i, musamman a kasar Habasha wadda ke da babban burin fitar da kayayyakinta zuwa kasashen waje, da samun kudaden musanya na ketare. Layin dogon na iya taimakawa ga bunkasuwar tattalin arzikin wurin sosai."

To, ko yaya tattalin arzikin wurin zai ci gaba da habaka sakamakon gina wannan layin dogo? Hakan na dogara ne kan yadda za'a gudanar da ayyukan kula da shi, gami da yadda gwamnatin wurin za ta aiwatar da harkokinsa bisa karfin kanta. A ganin kamfanin kiyayewa gami da kula da layin dogo tsakanin Habasha da Djibouti, ya zama dole a taimakawa gwamnatin wurin wajen inganta kwarewarta, kuma ya kafa wani sashi na musamman don samar da horaswa ga ma'aikatan wurin. Daga watan Fabrairun shekara ta 2018, ya zuwa yanzu, akwai ma'aikatan wurin kusan dari uku, wadanda suka samu horaswa game da ilimin jiragen kasa, al'amarin da ya kara jawo hankalin matasan wurin don su shiga cikin ayyukan kula da jiragen kasa.

Abrham Fenet ya fara aiki a rukunin kula da harkokin layin dogon, bayan da ya kammala karatunsa a jami'a a shekara ta 2018. A matsayin wani dan kasar Habasha wanda ke sha'awar al'adun kasar Sin, Abrham ya yi kokarin koyon yaren Sin, kuma yana fatan nuna himma da kwazo wajen koyon ilimin da ya shafi shimfida layin dogo, ta yadda zai kara bayar da gudummawarsa ga aikin raya kasarsa wato Habasha. Abrham Fenet ya ce:

"A halin yanzu akwai daliban jami'o'i da dama, wadanda ke fuskantar matsalar rashin ayyukan yi bayan da suka gama karatu a makaranta a Habasha. Alal hakika na yi sa'a sosai, saboda na iya shiga aikin gina layin dogo tsakanin Habasha da Djibouti bayan da na gama karatun jami'a. Babban fatana shi ne, ci gaba da samun ilimin da ya shafi layin dogo, da kara fahimtar al'adun kasar Sin, don bayar da gudummawata ga karfafa dankon zumunci tsakanin Habasha da Sin. Ina kuma fatan zan iya bada gudummawa gwargwadon karfina, ga ayyukan shimfida layin dogo na kasarmu a nan gaba."

Shi ma a nasa bangaren, mataimakin shugaban sashin kula da daukar ma'aikata na kamfanin kiyayewa gami da kula da layin dogo tsakanin Habasha da Djibouti, He Jiang ya bayyana cewa, yana fatan kasashen biyu wato Sin da Habasha za su ci gaba da yin hadin-gwiwa don kyautata wannan layin dogo. Mista He ya ce:

"Idan mun kammala wani aiki, dole ne mu taimaka ga aiwatar da shi da kulawa da shi, wannan shi ne aikin da muke yi yanzu, kuma babban buri ne da muke kokarin cimmawa a nan gaba yayin da muke shimfida layukan dogo. Mun taimaka ga shimfida layin dogo tsakanin Habasha da Djibouti, shi ya sa dole mu taimaka wajen taka muhimmiyar rawar cin nasararsa, ba za mu kyale ya lalace ba. Ya kamata mu yi iyakacin kokari don karfafa zumunci tsakanin Sin da Afirka."

Layin dogon da ya hada kasashen Habasha da Djibouti, shi ne irinsa na farko na zamani mai aiki da karfin wutar lantarki da kamfanonin kasar Sin suka taimaka wajen ginawa a nahiyar Afirka, wanda ya zama wani babban misali na hadin-gwiwa gami da zumunci dake tsakanin Sin da kasashen Afirka.

A shekaru shidan da suka gabata, wato a watan Maris din shekara ta 2013, yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke ziyarar aiki kasashen Afirka, ya bayyana muhimman manufofin da gwamnatin kasar Sin ke da su wajen aiwatar da hadin-gwiwa tare da kasashen Afirka, wato nuna gaskiya da sahihanci da aminci ga aminai kasashen Afirka, ciki har da taimakawa kasashen Afirka inganta muhimman ababen more rayuwar jama'arsu. Daga baya a watan Mayun shekara ta 2014, gwamnatin kasar Sin ta yi alkawarin taimakawa kasashen Afirka shimfida layukan dogo, don su cimma burin hada manyan biranen kasashen Afirka ta layin dogo, kuma layin dogo tsakanin Habasha da Djibouti na daya daga cikin irin wadannan layukan dogon da kasar Sin ta gina a nahiyar Afirka.

Idan mun dubi tarihi, a shekaru sama da arba'in da suka gabata, mutanen kasar Sin da na Afirka sun hada kai don shimfida wani shahararren layin dogo a Afirka, wato layin dogon da ya hada Tanzaniya da Zambiya, wanda ya shaida irin dadadden zumunci da hadin-gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Idan mun ce layin dogo tsakanin Tanzaniya da Zambiya ya shaida irin taimakon da kasar Sin ta baiwa kasashen Afirka wajen yaki da ra'ayin nuna wariyar launin fata, don Afirka ta samu 'yancin kai ta fannin siyasa, shi layin dogon da ya hada Habasha da Djibouti ya shaida irin goyon-baya da tallafin da gwamnatin kasar Sin ta baiwa Afirka don ta samu ci gaban tattalin arziki mai dorewa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China