in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yadda na'urar Chang'e-4 ta kasar Sin ta yi nasarar sauka a bayan duniyar wata
2019-01-10 14:20:36 cri

Da misalin karfe 10 da minti 26 na ranar 3 ga watan Janairun shekarar 2019 ne, na'urar bincike ta Chang'e-4 da kasar Sin ta kera ta sauka a bayan duniyar wata, sa'an nan, ta aiko wani hoton bayan duniyar wata zuwa duniyarmu ta tauraron dan adam na "Queqiao". Wannan shi ne hoton bayan duniyar wata na farko da wata na'urar da bil Adama ya kera ta dauka.

Wannan ci gaba ya nuna cewa, na'urar da kasar Sin ta kera ta sake sauka a duniyar wata, bayan chang'e-3 da ta sauka a duniyar wata a shekarar 2013. Kuma kasar Sin ta kasance kasa ta farko wadda ta yi nasarar harba na'urar bincikenta a gaba da kuma bayan duniyar wata. Wannan hakika wani babban ci gaba ne da bil Adama ya samu a fannin nazarin kimiyyar sararin samaniya.

Tun a ranar 8 ga watan Disamban shekarar 2018 ne, aka harba na'urar Chang'e-4 daga cibiyar harba taurarin dan Adam dake Xichang na kasar Sin, inda na'urar ta kama hanyar zuwa duniyar wata. An kera na'urar Chang'e-4 bayan na'urar Chang'e-3, wadda ta sauka a duniyar wata shekaru 6 da suka wuce. Daga bisani, masana kimiyya da fasaha na kasar Sin sun yi nazarce-nazarce kafin su yanke shawarar harba wannan na'urar, wadda da ma ba a yi niyyar harba ta.

Tsarin na'urar bincike ta Chang'e-4 ya yi kama da na Chang'e-3, amma sakamakon gangarar yanayin kasa dake bayan duniyar wata, da rashin hotunansa a zahiri, akwai matukar wuya da rashin tabbas ga aikin saukar na'urar bincike ta Chang'e-4. Don haka, masana kimiyyar kasar Sin suka yiwa na'urar kwaskwarima ta yadda zai dace da yanayin kasa da ma duniyar wata, lamarin da ya sa na'urar ta zama na'urar bincike ta farko a fadin duniya da ke iya sauka a bayan duniyar wata. Daga baya kuma, na'urar bincike ta Chang'e-4 za ta kara gudanar da bincike kan yanayin kasa da albarkatu na duniyar wata daga dukkanin fannoni, don kara ilimantar da dan Adam game da duniyar wata.

Tun bayan da kasar Sin ta harba na'urar bincike ta Chang'e-1 zuwa duniyar wata, kawo yanzu, Sin ta harba irin wadannan na'urori guda hudu. Na'urorin bincike guda uku da aka harba tun farko, sun sanya kara tabbatar da matakai biyu na gaba kan matakai guda uku na ayyukan binciken duniyar wata na kasar Sin, wato kewayen wata da kuma sauka a duniyar wata.

Don hakan, duniyar wata shi ne matakin farko ga dan Adam na yin rayuwa a sararin samaniya. Na'urar binciken duniyar wata kirar Chang'e-4 sabon mataki ne da dan Adam ya yi kokari wajen cimma wannan buri, kana ya shaida cewa, kasar Sin ta yi kokari wajen raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama. (Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China