in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Don Me Shugaba Xi Jinping Ya Yaba Wa Dattijo Ma?
2019-02-11 09:34:17 cri

A watan Disamban shekarar 2018, a yayin da kwamitin kolin jam'iyyar kwamnis ta kasar Sin da gwamnatin kasar suke shirya taron murnar cika shekaru 40 da suka gabata tun bayan fara aiwatar da manufar bude kofarta ga ketare da kuma yin gyare-gyare a gida, an yaba wa nagartattun mutane 100 wadanda suka bayar da muhimmiyar gudummawa ga ci gaban kasar Sin cikin wadannan shekaru 40 da suka gabata.

Daya daga cikinsu, akwai dattijo Ma Shanxiang wanda ya samu amincewa daga wajen jama'a, da kuma gwamnati wajen daidaita rikice-rikicen dake kasancewa tsakanin jama'a. Kuma shugaban kasar Sin, kana babban sakataren kwamitin koli JKS Xi Jinping ya yaba masa. A cikin shekaru da suka gabata, dattijo Ma wanda yake mai da hankalinsa sosai wajen didaita ringingimu da matsalolin dake kasancewa tsakanin jama'a ya samu wasu "fasahohin daidaita matsala". Ana yabawa fasahohinsa sosai. A cikin shirinmu na yau, bari mu gabatar muku da labari na 7 na "Yadda shugaba Xi ya yaba wa dattijo Ma" da ke cikin jerin Labarai kan yadda shugaba Xi Jinping yake kulawa da zaman rayuwar fararen hula.

"Ni ne Ma Shanxiang. Ina da wani ofis a titin Guanyinqiao dake birnin Chongqing, inda na yi shekaru 30 ina kula da harkokin fararen hula, har ma yawan littattafan da na rubuta game da harkokin da na taba daidaitawa ya kai fiye da 160. Yawan fasahohin da na samu wajen daidaita ringingimu da matsalolin dake kasancewa tsakanin fararen hula ya kai fiye da 60……"

A wani taron wakilan jama'ar kasar Sin da aka shirya a watan Maris na shekarar 2018, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarta, dittijo Ma Shanxiang ya yi wani bayani, inda ya bayyana yadda yake yin aikin daidaita matsalolin da jama'a fararen hula suke fuskanta.

A shekarar 1988, Ma Shanxiang ya yi ritaya daga rundunar soja, ya kuma fara yin aikin daidaita ringingimu da matsaloli tsakanin fararen hula a titin Guanyinqiao na birnin Chongqing. A cikin shekaru 30 da suka gabata, ya dukufa ka'in da na'in wajen taimakawa fararen hula daidaita matsalolin da suke fuskanta, ya kuma ci nasarar daidaita ringingimu dake kasancewa tsakanin fararen hula har fiye da sau 2000. Yanzu, ko da yake shekarunsa sun isa lokacin yin ritaya, yana ci gaba da bayar da gudummawarsa a "Ofishin Dattijo Ma" dake titin Guanyinqiao. A cikin shekaru da dama da suka gabata, dattijo Ma ya kafa ka'idojin yin aikinsa kamar yadda ake fata, wato, a tashi a yi maraba da zuwan wanda ya gamu da matsala, sannan ya gayyace shi ya zauna ya ba shi ruwan sha. Dole ne a rubuta koke-koken da aka gaya masa, da yin musayar ra'ayoyi kan yadda za a iya kawar da koke-koke da kuma matsalolin da yake fuskanta. Daga karshe dai, ya yi ban kwana a wajen kofar ofishinsa. Dattijo Ma Shanxiang ya ce, dole ne a samu batu mafi muhimmanci dake da alaka da matsalolin da fararen hula suke fuskanta, ta yadda za a iya kawar da su gaba daya.

"Mu kan gamu da wasu matsaloli da rikice-rikicen da fararen hula suke fuskanta. Alal misali, matsalar rushe tsoffin gidajen kwana, batutuwan tafiyar da harkokin yau da kullum a birninmu, da matsalolin dake kasancewa tsakanin mazauna unguwa, da kamfanin dake da nauyin kulawa da unguwar, har ma matsalar rarraba dukiyoyi tsakanin iyali da dai makamatansu. Dole ne mu kware sosai wajen daidaita su yadda ya kamata. Nauyin dake bisa wuyanmu shi ne, a lokacin da muke neman ci gaban kasarmu, dole ne mu mai da hankali kan yadda za a iya saka jituwa tsakanin fararen hula, da kuma tsakaninsu da hokumomin gwamnati."

Yanzu, fasahohin da dattijo Ma ya samu sun zama misalai ga wadanda suke aiki a kananan hukumomin kasar Sin. Da ya tashi daga ofis, dattijo Ma ya kan ba da horo ga sabbin ma'aikatan kananan hukumomin birnin Chongqing a wasu unguwanni. Haka kuma, ya kan shiga jami'o'i domin koyar da dalibai tunanin Kwaminisanci, har ma ya tafi can yankunan karkara domin sanar wa manoma manufofi, da matakan da gwamnati, da kuma kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin suke dauka, domin kawar da matsalolin da fararen hula ko manoma suke fuskanta. Dattijo Ma ya kara da cewa, "A matsayin wani dan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, idan kana kishin jam'iyyarka da kuma jama'a, tabbas ne za ka samu maraba da karba hannu bibbiyu a ko'ina."

Jawabin da Ma Shanxiang ya gabatar ya girgiza shugaba Xi Jinping. Shugaba Xi ya ce, "Duk da yake akwai dimbin hukumomi a sama, amma dole ne wani ya sauke nauyin da aka dora wa kananan hukumomi. Dole ne mu karfafa tushen ayyukan da kananan hukumomi suke yi. Idan babu kananan hukumomi masu karfafa, ba za a samu kwanciyar hankali ba. Muna bukatar dimbin kananan jami'ai kamar dattijo Ma a kananan hukumomi. Ina fatan dattijo Ma zai ci gaba da yin aikinsa kamar yadda ake fata, har ya sake samun kyakkyawan sakamako."

A lokacin da yake halartar taron wakilan jama'ar kasar Sin a nan Beijing, dittijo Ma ya rubuta ra'ayoyinsa da wasu abubuwan da ya gani da idonsa a cikin wani littafinsa. Ya ce, tabbas ne yaba masa da shugaba Xi ya yi ya sa masa kaimi matuka. Dole ne ya yi kokarin koyo da kuma mallakar manufofi da matakan da kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ke dauka, ta yadda zai iya inganta aikinsa na bautawa al'umma. Dattijo Ma yana mai cewa, "Lokacin da muka yi hannu, shugaba Xi ya yaba min yana cewa, jawabin da na bayar yana da kyau sosai. Ina alfahari da yabon da shugaba Xi ya yi min."

To, wannan shi ne labari game da yabon da shugaba Xi na kasar Sin ya yiwa dattijo Ma. Har yanzu, dattijo Ma yana ci gaba da bautawa mazauna unguwa inda yake aiki. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China