A madadin babban jami'in rundunar wanzar da tsaron kasa ta National Bolivarian Armed Forces (FANB), Padrino ya bayyana cewa, Trump "sama sam ba ya mutunta 'yancin kasarmu a matsayinta na jamhuriya (ta juyin juya hali), da nuna adawa da mulkin danniya da kuma yanayin tafiyar da ayyukan hukumomin kasarmu."
A cikin jawabin da ya gabatar a ranar Litinin ga wasu dandazon 'yan gudun hijirar Venezuela a yankin Miami, na jahar Florida, Trump, ya zargi shugaban kasar Venezuelan Nicolas Maduro da jagorancin gwamnatin 'yan gurguzu ta kama karya.
Trump ya kuma bukaci jami'an dake goyon bayan Maduro dasu bada damar shigar da kayayyakin jin kan al'umma, kana ya bukaci dakarun tsaron kasar dasu amince da tayin da 'yan adawa suka yi na neman afuwa, idan ba haka ba, komai zai iya lalacewa. (Ahmad)