in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Birtaniya ta ci babbar gajiya bisa kasancewar cibiyar cinikayya da kudin Sin RMB
2019-02-20 16:08:04 cri

Tun bayan watan Yulin shekarar 2018 da ta gabata, tattalin arzikin kasar Sin bai samu ci gaba cikin sauri kamar yadda ake fata ba, haka kuma shawarwarin cinikayyar dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka bai samu sakamako mai gamsarwar ba, a don haka wasu kasashen duniya suka nuna shakku kan amfanin kudin Sin RMB a kasuwar jarin duniya, amma Birtaniya wadda babbar kasa ce ta tafiyar da harkar kudi tana cike da imani kan RMB, har ta ci babbar gajiya daga wajen. Bisa labarin da aka bayar a kan shafin yanar gizo na jaridar "Financial Times" ta Birtaniya, an ce, ya zuwa karshen bara, adadin cinikayya da kudin Sin RMB ya zarta cinikayya tsakanin Fam na Birtaniya da kudin Euro, kana alkaluman bankin Ingila sun nuna cewa, matsakaicin adadin cinikayya da kudin Sin RMB a kowace rana a watan Oktoban bara ya kai dalar Amurka biliyan 73, lamarin da ya nuna cewa, ban da kasar Sin, Birtaniya ta kasance cibiyar cinikayya da kudin Sin RMB mafi girma a fadin duniya.

A shekarar 2012, birnin London ya kaddamar da shirin raya cibiyar cinikayya da kudin RMB a birnin. A sa'i daya kuma, kasar Singapore da birnin Paris na kasar Faransa da birnin Frankfurt na kasar Jamus da ma kasar Luxembourg suna kokarin raya cibiyoyin cinikayya da kudin RMB. A cikin takararsu a wannan zagaye, ba Birtaniya ce kasa ta farko da ta kaddamar da shirin ba, amma bisa hangen nesa da take da shi da ma kokarin sa kaimi ga shirin, ta nuna fifiko a bayyane, har ma ta zama cibiyar cinikayya da kudin RMB mafi girma a duk duniya.

Alkaluman kungiyar kasa da kasa dake samar da bayanan hada-hadar kudi ga bankuna wato SWIFT sun nuna cewa, a watan Disambar bara, sama da kashi 36 bisa dari na cinikin da aka yi da kudin Sin RMB, an yi su ne a kasar Birtaniya, kana, cinikin da aka yi da kudin Sin a Faransa da Singapore ya kai kashi 6 bisa dari. Cinikin da ake yi da kudin Sin RMB ya samu saurin bunkasuwa a Birtaniya saboda mu'amalar tattalin arziki da kasuwanci tsakanin Sin da Birtaniya. Kididdigar ma'aikatar kudin Birtaniya ta yi nuni da cewa, Birtaniya ta riga ta zama kasuwa mafi saurin bunkasuwa a nahiyar Turai, inda ake amfani da kudaden RMB don saye da sayarwa. Daga watan Janairu zuwa Agustan shekarar da ta gabata, kudin cinikayyar da aka yi da kudin Sin RMB tsakanin Sin da Birtaniya ya kai Yuan biliyan 250, adadin da ya karu da kashi 150 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin shekarar ta 2017, kuma cinikin da aka yi da RMB ya dauki kashi 20 bisa dari na dukkan cinikin kayayyaki da aka yi.

Ba sabon abu ba ne yin ciniki da amfani da kudin Sin RMB a kasar Birtaniya. A shekarun baya bayan nan, an aiwatar da sabbin matakan hada-hadar kudi a kasar Sin da kasar Birtaniya. A shekarar 2014, gwamnatin kasar Birtaniya ta gabatar da takardun bashi na kudin Sin RMB na tsawon shekaru 3 karo na farko, darajarsu ta kai kudin Sin RMB Yuan biliyan 3. Wannan ne karo na farko da kasar yammacin duniya ta gabatar da takardun bashi na RMB, kana darajarsu ta fi yawa a kasashen duniya ban da wanda aka gabatar da su a cikin kasar Sin, don hakan sun jawo hankalin masu zuba jari na kasashen waje sosai. Tare da aiwatar da bude kofar kasuwar jari ta kasar Sin ga kasashen waje, Sin da Birtaniya sun tsai da kudurin bayar da takardun iznin yin ciniki a tsakanin Shanghai da London, ta hakan kamfanonin birnin Shanghai da na London da suke da sharuda da aka tsara su na iya yin amfani da wadannan takardun izni wajen yin ciniki a kasuwar bangarorin biyu, kuma za a kara bude kofa ga juna wajen yin ciniki a tsakaninsu.

Ko da yake a kusan shekara guda da ta wuce, wasu kasashe sun ce, kasar Sin na fuskantar koma bayan tattalin arzikinta, amma an gaggauta amfani da RMB a harkokin duniya a shekarar 2018. Bisa kididdigar da babban bankin kasar Sin ya bayar, a shekarar 2018 jimilar kudin RMB da ake amfani da su wajen cinikayyar ketare ta kai yuan triliyan 5.11, jimilar RMB da ake amfani da su wajen zuba jari kai tsaye ta kai triliyan 2.66. A hannu guda, bayan da aka shigar da RMB cikin jerin kudade bisa tsarin SDR na kungiyar IMF, kasar Sin ta riga ta sanya hannu kan yarjejeniyoyin musayar kudi tare da kasashe sama da goma, har ma kasashe da yankuna fiye da sittin suka mai da RMB matsayin kudin musaya da aka tanada, kasashe da kamfanonin ketare dake amfani da RMB wajen musaya da biya kudi sun yi ta karuwa.

Bude kofar kasuwar hada-hadar kudi da gaggauta fadada wurare masu yin amfani da kudin Sin RMB, su ne manyan bangarori ga manufar gwamnatin kasar Sin ta gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje. Saboda haka, birnin London bisa matsayinsa na babbar cibiyar sarrafa kudin Sin RMB, tana kokarin yin amfani da wannan dama. Yanzu abin da za a iya hasashensa shi ne, bisa karfin tattalin arzikin Sin, da makudan kudin kasashen waje da ta ajiye, darajar kudin RMB za ta kara zama cikin wani yanayi mai karko, sa'an nan za a fara yin amfani da kudin a karin kasashe daban daban. Aikin raya kasuwar kudin RMB a kasashen waje wani muhimmin bangare ne ga sana'ar hada-hadar kudin kasar Sin, wanda zai taimakawa yaduwar kudin RMB, da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya". Ban da haka kuma, zai zama wani babban zarafi mai kyau ga kasar Sin da sauran kasashe masu alaka da lamarin. (Jamila Kande Murtala Zainab Bilkisu Bello)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China