in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD ya nada sabon kwamandan rundunar wanzar da zaman lafiya a yammacin Sahara
2019-02-21 09:17:26 cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya sanar a jiya Laraba cewa ya nada manjo janar Zia Ur Rehman dan kasar Pakistan a matsayin sabon kwamandan rundunar wanzar da zaman lafiya ta MDD a yammacin Sahara wato (MINURSO).

Ur Rehman zai maye gurbin manjo janar Wang Xiaojun dan kasar Sin, wanda wa'adin aikinsa ya cika a ranar 17 ga watan Fabrairu. Wata sanarwar da kakakin mista Guterres ya fitar ta ce, babban sakataren yayi matukar farin ciki bisa namijin kokarin da kwamanda Wang ya nuna musamman wajen sadaukar da kai don bada gudunmowa ga ayyukan tawagar tsaro ta MINURSO.

Ur Rehman yana da kwarewar aiki na shekaru 30, a matakin kasa da kuma na kasa da kasa game da tafiyar da harkokin soji, ya rike matsayin kwamandan rundunar sojoji da kuma daraktan daukar ma'aikata a rundunar sojoji, da kwalejin horas da dabarun yaki.

An raba yankin yammacin Sahara tsakanin Morocco da Mauritania bayan kawo karshen mulkin mallakar kasar Sifaniya a shekarar 1976. A lokacin da Mauritania, ke karkashin matsin lamba daga Polisario guerrillas, inda ta janye dukkan korafe korafenta game da mallakar yankunan a watan Augastan 1979, Morocco ta cigaba da mamaye yankunan inda ta kafa hukumar dake kula da dukkan yankunan da ake takaddama kan su. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China