in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za'a zamanantar da koyarwar makarantun sakandaren Kamaru: inji minista
2019-02-21 10:07:11 cri
Ministar kula da ilmin sakandare ta jamhuriyar Kamaru Nalova Lyonga, ta ce kasar zata fara koyar da daliban makarantun sakandare ta hanyar intanet domin kyautata tsarin koyo da koyarwa a kasar.

"Muna da makarantu masu yawa wadanda ba'a gina su bisa tsarin koyarwar da ya kamata ba. Muna neman hanyoyin dabarun koyarwa. Muna son mu koma tsari na zamani," Lyonga ta bayyana hakan ne a lokacin taron bibiyar ayyukan ilmi na tsakiyar zango na shekarar 2018-2019 wanda aka gudanar a Yaounde.

"Saka karin darrusan da muke da su kan yanar gizo ta intanet zai fi ba da ma'ana, kuma ta wadannan dabarun ne za mu iya mayar da darasin mintuna 45 zuwa minti 10 ta hanyar bayyana muhimman abubuwan da darasin ya kunsa", in ji ta.

Tuni jamhuriyar Kamaru ta fitar da wani samfuri na tsarin koyarwa ta intanet, kuma an fara horas da malamai game da yadda za su tafiyar da aikin, in ji jami'ar. Ta kuma kara da cewa, shirin zai shafi makarantun sakandare 2,000 ne a fadin kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China