A wata sanarwar da AU ta fitar ta ce, rundunar tsaron hadin gwiwar ta bukaci gwmanatin Mali ta rubanya kokarinta wajen shawo kan tabarbarewar yanayin tsaron da ake fuskanta a kasar, tare da hadin gwiwar da masu tallafawa shirin wanzar da zaman lafiyar a kasar.
Hukukomin biyu sun yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su jajurce wajen tabbatar da ganin an dauki matakan aiwatar da yarjejeniyar hana yaduwar makamai da wayar da kan al'umma kan tabbatar da zaman lafiya.
Tawagar hadin gwiwar ta kara nanata kira ga kasa da kasa dasu tallafawa shirin hadin gwiwar na wanzar da zaman lafiyar na dakarun kiyaye zaman lafiya na MDD a Mali (MINUSMA).(Ahmad Fagam)