in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kafa cibiyar gwajin na'urori masu kwaikwayon tunanin dan Adam a Beijing
2019-02-21 11:15:30 cri
Kwamitin kimiyya da fasaha na birnin Beijing ya sanar a jiya Laraba cewa, an kafa wata cibiyar gwajin na'urori masu kwaikwayon tunanin dan Adam, wadda ta kasance irinta na farko da aka samu a kasar Sin.

A wannan sabuwar cibiyar, za a yi kokarin samar da sabbin fasahohi masu alaka da na'urori masu amfani da fasaha da kansu, da gwajin amfani da su. Ta haka, ana sa ran maida birnin Beijing ya zama kan gaba a duniya wajen mallakar fasahohi, da kwararru, gami da daidaituwar manufa, a fannin fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam.

Da ma dai birnin Beijing yana da fifiko wajen kirkiro sabbin fasahohi masu alaka da na'ura mai kwaikwayon tunanin dan Adam, musamman ma a fannonin manufar gwamnati, kwararru, da masana'antu. Daga bisani gwamnatin wurin ta kara daukar wasu matakai cikin shekarun nan, don tallafawa sana'ar daga dukkan bangarori. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China