in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Trump: Za a kara ganawa da shugaban Koriya ta Arewa
2019-02-21 11:17:16 cri
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya fada a jiya Laraba cewa, bayan ganawar da zai yi da shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong-un a Hanoi na kasar Vietnam, yana shirin kara ganawa da takwaransa na Koriya ta Arewa.

Shugaban na Amurka ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da Sebastian Kurz, firaministan kasar Austria, wanda ke ziyara a kasar Amurka, inda shugaba Trump ya ce, ganawarsa da Kim Jong-un ta wannan karo ba zata zama ta karshe ba. A cewarsa, zai iya soke takunkumin da aka sakawa Koriya ta Arewa, sai dai ana bukatar kasar ta dauki wasu matakai " masu ma'ana". (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China