in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci kwamitin sulhun MDD ya yi la'akari da sake tattauna ayoyin kudurin doka da aka yiwa gyaran fuska game da takunkumin da aka sakawa Koriya ta Arewa
2019-02-21 20:31:38 cri
Game da kalaman shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi kwanakin baya na duba yiwuwar da sassauta takunkumin da aka sakawa kasar Koriya ta Arewa, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana a yau Alhamis cewa, bisa halin da ake ciki, Sin tana ganin cewa akwai bukatar kwamitin sulhun MDD ya yi la'akarin sake tattauna ayoyin kudurin doka da aka yiwa gyaran fuska game da takunkumin don nuna goyon baya ga warware matsalar ta hanyar siyasa.

A yayin taron manema labarun da aka gudanar a yau, Geng Shuang ya jaddada cewa, Sin ta nuna goyon bayan Koriya ta Arewa da Amurka da su kiyaye yin shawarwari da ma cimma matsaya, tare da fatan za a gudanar da ganawa ta karo na biyu a tsakanin shugabannin Koriya ta Arewa da Amurka yadda ya kamata da ma samun kyakkyawan sakamako. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China