in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Nijeriya ta fuskar tattalin arziki da ciniki a Abuja
2019-04-17 10:49:55 cri

An gudanar da taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Nijeriya ta fuskar tattalin arziki da ciniki dangane da shawarar "ziri daya da hanya daya" jiya Talata a birnin Abuja, hedkwatar kasar Nijeriya.

A cikin jawabinsa yayin taron, Zhao Yong, mukaddashin jakada na wucin-gadi a ofishin jakadancin kasar Sin a Nijeriya ya ce, za a bude taron dandalin tattaunawar koli ta yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa dangane da shawarar "ziri daya da hanya daya" karo na 2 a karshen wannan wata a Beijing, inda mutane kimanin dubu daya daga kasashe 148, ciki had da Nijeirya da kuma kungiyoyin kasa da kasa za su halarta. Ya ce, an yi imanin cewa, taron dandalin tattaunawar zai kasance wata ishara wajen raya shawarar ta "ziri daya da hanya daya" cikin hadin gwiwa.

Ernest Afolabi, mataimakin ministan harkokin kasafin kudi da tsare tsare na kasar Nijeriya, ya jaddada a yayin taron cewa, shawarar "ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta gabatar ta kawo wa kasashen duniya alheri baki daya. Kana ta bai wa Nijeriya kyakkyawar damar kara azama kan yin ciniki da jawo jari daga waje. Ya kara da cewa, ci gaban fasaha ya sa kaimi ga bunkasar tasoshin jiragen ruwa, filayen jirgin sama, hanyoyin dogo da hanyoyin mota a Nijeriya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China