Sanarwar ta bayyana cewa, dakatar da aikin nuna adawar mataki ne da kungiyar SPLM-North ta dauka don daidaita batun kasar Sudan cikin lumana, hakan zai taimakawa mika ikon kasar ga gwamnatin fararen hula.
Sojojin gwamnatin kasar Sudan sun yi yake-yake da kungiyar SPLM-North tun daga shekarar 2011. A watan Yuni na shekarar 2016, shugaban kasar Sudan na lokacin Omar al-Bashir ya sanar da cewa, sojojin gwamnatin kasar sun tsagaita bude wuta har na tsawon watanni 4. Bayan hakan, gwamnatin kasar Sudan ta tsawaita wa'adin tsagaita bude wuta a yankunan dake tinkarar rikice-rikice sau da dama. Kana kungiyoyi masu adawa da dama su ma sun sanar da tsagaita bude wuta a kasar. (Zainab)