in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta bunkasa samar da kudaden tallafi ga kananan sana'o'i
2019-04-18 10:56:27 cri

Majalissar gudanarwar kasar Sin, ta kaddamar da wasu sabbin matakai na kara bunkasa kananan sana'o'i, ta hanyar samar da tallafin rance da rage kudin ruwa ga masu kananan kamfanoni.

A jiya Laraba ne dai majalissar ta yi zamanta karkashin jagorancin firaminista Li Keqiang, inda ta amince da sabbin matakan samar da karin kudade, da fadada samar da guraben ayyukan yi, da ingiza harkokin ci gaba.

Wata sanarwa da majalissar ta fitar bayan taron, ta ce matakin samar da bashi mai sauki, da kara rage bashin da za a biya, da samar da karin dokokin da za su saukaka wa kanana da matsakaitan bankuna gudanar da hada hadar kudi, ta hanyar rage adadin kudaden ajiya, za su taimaka matuka a wannan fanni.

Sanarwar ta jaddada aniyar gwamnati, ta samar da bashi da yawan sa ya kai kudin kasar yuan biliyan 200, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 30, domin cin gajiyar kanana da matsakaitan sana'o'i da yawan su ya kai 100,000 a wannan shekara ta 2019.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China