in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Rasha ya yi kira da a gaggauta kafa kwamitin tsarkake mulkin Syria
2019-04-18 11:34:30 cri
A jiya Laraba, ministan harkokin wajen kasar Rasha, Sergei Lavrov, ya yi kira da a gaggauta kafa wani kwamitin tsarkake mulki a kasar Syria.

Ban da haka, mista Lavrov ya yi kira ga MDD da ta tsaya kan matsayin da ta tabbatar da shi a wani kudurinta mai lamba 2254, sa'an nan kar ta karbi ra'ayi na wasu kasashe na hana gudanar da "Shirin Astana". Domin "shirin Astana shiri ne daya tilo da zai taimakawa daidaita batun Syria", in ji ministan kasar Rasha.

Kafin haka, kwamitin sulhun MDD ya zartas da kuduri mai lamba 2254 a watan Disamban shekarar 2015, inda aka jaddada wasu manufofi na girmama mulkin kan kasar Syria, da 'yancin kanta, da dinkewar kasar waje guda, gami da kare cikakken yankinta. Sa'an nan za a ba jama'ar kasar cikakkiyar damar tabbatar da makomar kasar, inda za a sa kaimi ga bangarorin kasar don su yi masalaha, sa'an nan su nemi wata hanyar daidaita maganar kasar wadda kowa zai yarda da matakin.

A shekarar 2017, kasashen da suka hada da Rasha, da Turkiya, da Iran, sun kaddamar da shirin Astana, don samar da wani tsari na yin shawarwari don daidaita batun Syria. Bisa wannan tsari, masu ruwa da tsaki sun riga sun kira tarukan kasa da kasa da dama. Sa'an nan a watan Janairun shekarar 2018, an yi taron shawarwari na kasar Syria a Sochi na kasar Rasha, inda aka yanke shawarar kafa kwamitin tsarkake mulki a kasar Syria. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China