in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cimma nasara bisa matakin farko kan wasu ayyukan hadin kai tsakanin Sin da Afirka game da shawarar "Ziri daya da hanya daya"
2019-04-18 20:11:29 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya ce, ya zuwa yanzu kungiyar AU da wasu kasashen Afirka su 37 sun riga sun sanya hannu kan yarjejeniyar hadin kai da kasar Sin game da raya shawarar "Ziri daya da hanya daya". An kuma soma gudanar da manyan ayyukan hadin kai da dama a tsakanin Sin da Afirka bisa tsarin shawarar "Ziri daya da hanya daya", kana an samu nasara a matakin farko.

Kakakin ya bayyana haka ne a yayin taron manema labaru da aka shirya a yau Alhamis, inda ya kara da cewa, za a shirya taron kolin tattaunawar hadin kan kasa da kasa game da shawarar "Ziri daya da hanya daya" karo na 2 a nan brining Beijing ba da dadewa ba, inda ake fatan shugabanni da manyan wakilai daga kasashen Afirka da dama za su halara. Kasar Sin tana fatan hada kai tare da kasashen Afirka, don tabbatar da nasarorin da aka cimma a taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka da aka gudanar bara a birnin Beijing, da aikin raya shawarar "Ziri daya da hanya daya" tare tsakanin Sin da Afirka, da ajandar AU game da raya nahiyar Afirka nan da shekarar 2063, da ajandar neman dauwamamman ci gaba na MDD kafin shekarar 2030, da kuma manyan tsare-tsare raya kasashe daban daban na Afirka, da nufin inganta hadin kan su a fannonin raya sana'o'i, gina mayan kayayyakin more rayuwa, zuba jari da cinikayya da dai sauransu, kana da inganta rayuwar al'ummar Afirka, ta yadda za a kara samar da gajiya ga kasashen Afirka sakamakon ci gaba, da kara kawo moriya da alheri ga jama'ar Sin da Afirka. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China