in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kama wasu baki 4 da ake zargi da laifin satar mai a Nijeriya
2019-04-19 09:36:57 cri
An kama mutane 9 ciki har da baki 'yan kasashen waje 4, da ake zargi da satar man fetur a Lagos cibiyar hada-hadar kasuwanci ta Nijeriya.

Wani kwamandan sojin ruwa Dickson Olisemenogor, ya shaidawa manema labarai yayin da yake mika mutanen ga 'yan Sanda a Lagos cewa, an kama mutanen da suka hada da 'yan kasar Girka 3 da Ba'amuruke 1 da kuma 'yan Nijeriya 5 ne cikin jirgin ruwan SEA ANGELS 3, yayin wani samamen soji mai taken 'Junction Rain".

Kwamnadan ya ce an kama mutanen ne saboda zargin da ake musu na mallakar makamai da satar danyen man fetur.

Ya ce binciken da aka yi a jirgin ya gano bindigogi samfurin MI guda 4 da tarin alburusai 1,000 da kuma kayayyakin soji daban daban.

Kwamandan ya ce za a mika jirgin ruwan da wadanda ake zargin ga hukumomi domin gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China