in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalissar soji ta rikon kwarya a Sudan ta ce ba juyin mulki ta yi ba
2019-04-19 09:41:14 cri
Majalissar soji ta rikon kwarya dake jagoranci a kasar Sudan, ta ce kawar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Omar Al-Bashir ba juyin mulki ba ne, illa dai wani mataki na amsa kiran al'ummar kasar.

Wata sanarwa da kwamitin siyasa na majalissar ya fitar a ranar Alhamis, ta ce aikin majalissar shi ne jagorantar kasar kafin lokacin da za a kafa zababbiyar gwamnati.

An fitar da sanarwar ne dai, bayan kammala zaman tattaunawa tsakanin sashen siyasa da na sojin kasar da wakilan kungiyoyi da hukumomin kasa da kasa dake ayyukan su a cikin kasar.

Yayin zaman an gudanar da shawarwari da suka jibanci batun tsaro, da na siyasa, da ma batun kafa gwamnatin farar hula, da tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki a fannin siyasar kasar.

Tuni dai majalissar ta soji karkashin jagorancin shugaban ta Abdel-Fattah Al-Burhan, ta fara daukar wasu matakai masu nasaba da bukatun masu zanga zangar a sassan kasar ta Sudan. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China