in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dandalin ziri daya da hanya daya zai kara bunkasa samar da ababen more rayuwa a Habasha in ji wani masani
2019-04-19 09:57:42 cri
An bayyana dandalin tattaunawa game da shawarar ziri daya da hanya daya da za a gudanar nan da 'yan kwanaki a nan birnin Beijing, a matsayin wata kafa ta kara bunkasa samar da ababen more rayuwa a Habasha.

Shaihin malami, kuma masani a fannin tattalin arziki Costantinos Bt. Costantinos, shi ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Mr. Costantinos, wanda ya taba kasancewa mashawarci ga kungiyar AU, da hukumar MDD mai lura da raya tattalin arzikin Afirka ko ECA, ya ce sama da ko wace kasa a nahiyar Afirka, Habasha ce kan gaba wajen cin gajiyar shawarar ziri daya da hanya daya, musamman idan aka yi duba da layin dogo na Addis Ababa zuwa kasar Djibouti da aka gina karkashin wannan shawara, da ma sauran manyan ayyukan raya kasa.

Masanin ya kuma bayyana cewa, dandalin da za a gudanar a birnin Beijing, zai zamo wata hanyar karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban karkashin inuwar shawarar ta ziri daya da hanya daya.

Kalaman na Costantinos na zuwa ne, a gabar da gwamnatin kasar Habasha ke cewa, ta shirya halartar dandalin, da wata muhimmiyar tawaga wadda za ta kunshi firaministan kasar Abiy Ahmed, da sauran manyan wakilan gwamnati.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China