in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin Standard Chartered ya bayyana goyon bayan sa ga shawarar ziri daya da hanya daya
2019-04-19 10:26:29 cri
Wakilan bankin Standard Chartered sun bayyana goyon bayan su ga shawarar ziri daya da hanya daya, suna masu bayyana ta a matsayin wata dama ta bunkasa hada hadar cinikayya da tattalin arziki.

Yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya Alhamis, lokacin tsaren karba karba da aka shirya domin yayata manufar shawarar ziri daya da hanya daya a kasar Ghana, daya daga manyan daraktocin bankin Mr. Jerry Agyeman-Boateng, ya ce bankin sa na jinjinawa wannan shawara, duba da yadda take kokarin dinke sassan duniya ta fannin cinikayya.

Agyeman-Boateng ya ce bankin Standard Chartered, ya dauki wasu Sinawa aiki a mataki na manajoji, a rassan sa 44 dake sassan duniya, saboda irin amincewa da bankin yayi da shawarar ziri daya da hanya daya.

Ya ce sakamakon hakan, banki na iya baiwa kamfanonin kasar Sin shawarwari game da dabarun kaucewa matsalolin al'adu da yaruka da suka iya fuskanta, yayin da suke gudanar da harkokin su. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China