Da yake jawabi ga manema labarai a harabar ofishin jakadancin kasar Sin dake birnin Addis Ababa, Tan Jian ya ce taro kan shawarar Ziri Daya da Hanya Daya domin hadin giwar kasa da kasa da zai gudana a karshen watan nan a Kasar Sin, wani karfi ne da zai kara karfafa kawance tsakanin kasahsen biyu.
Ya ce hadin gwiwa kan shawarar ba zaman muhawara ba ce, yana mai cewa shiri ne da ya fi mayar da hankali kan aiwartar da ayyukan dake haifar da kyawawan sakamako. Ya ce bangarorin da za su halarci taron za su dora ne a kan nasarorin da aka samu, tare da kirkiro wasu ayyukan karkashin hadin gwiwar a matakai daban daban da za su kawo karin sakamako masu inganci.
Tan Jian ya ce Habasha na daya daga cikin kasashe 124 da suka sanya hannu kan hadin gwiwa da kasar Sin karkashin shawarar, ya na mai jaddada kudurin kasar Sin na marawa Habasha baya wajen taka muhimmiyar rawa a fannin yayata shawarar a nahiyar Afrika.
Jakadan ya kuma bayyana cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Habasha za ta ci gaba da bunkasa tare da zama abun koyi a tsarin shawarar. (Fa'iza Mustapha)