in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana da imanin cimma burin neman ci gaba, kuma za ta kara sassauta yanayin cinikin waje
2019-04-19 11:49:16 cri

A wani taron manema labaru da aka shirya jiya Alhamis a nan birnin Beijing, kakakin kwamitin bunkasa da yin kwaskwarimar kasar Sin ya bayyana cewa, a cikin farkon rubu'in bana, tattalin arzikin kasar Sin na samun ci gaba kamar yadda ake fata. Sannan, a wannan farkon rubu'in bana, yawan jarin da gwamnatin kasar ta kebe wa gwamnatocin matakai daban daban na larduna daga baitulmali ya riga ya kai 80% bisa jimillar jarin da za ta kebe musu a duk shekara. Sakamakon haka, babu shakka, kasar Sin na cike da imani da sharudda, da kuma karfi na cimma burin neman ci gaban tattalin arziki da zaman al'umma da ta kafa a farkon shekarar. A jiya kuma, wata jami'ar hukumar kula da kudaden musaya ta kasar Sin ta bayyana cewa, yanzu, ana amfani da jari tsakanin kasar Sin da sauran sassan duniya kamar yadda ya kamata, sannan kudaden musaya da aka adana a kasar Sin sun karu kadan. Wannan jami'a ta ce, hukumarta za ta ci gaba da yin kwazo da himma wajen inganta yanayin cinikin waje da kuma sassauta sharudan zuba jari. Yanzu ga wani rahoton da abokin aikinmu Sanusi Chen ya hada mana.


Bisa alkaluman da hukumar kasar Sin ta bayar kwanan baya, an ce, a farkon rubu'in bana, saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya kai 6.4% bisa makamancin bara, a yayin da yawan guraban aikin yi da farashin kayayyaki da yawan kudin musaya da aka adana a kasar Sin suke gudana kamar yadda ya kamata. Bugu da kari, yanzu sana'o'in tattalin arzikin kasar Sin sun samu ingantuwa sosai a lokacin da wasu sabbin sana'o'i da masana'antun fasahohin zamani da na ba da hidimomi suke samun bunkasa cikin sauri.

A yayin taron manema labaru da aka shirya a wannan rana, Mr. Yuan Da, kakakin kwamitin bunkasa da yin kwaskwarimar kasar Sin ya bayyana cewa, a lokacin da ake kara yin gyare-gayare da bude kofarta ga ketare, a bayyane ne yanzu yanayin kasuwancin kasar Sin ya samu ingantuwa sosai. Mr. Yuan Da yana mai cewa, "Yanzu ana karfafa yin gyare-gyare kan wasu hidimomin da hukumomin gwamantin ke samarwa, sakamakon haka, yanayin kasuwancin kasar ya samu ingantuwa sosai. Sannan a karo na hudu, yanzu ana hanzarta gwajin yin gyare-gyare kan wasu manyan masana'antu mallakar gwamnati. Bugu da kari, bisa shawarar 'ziri daya da hanya daya', ana habaka fannonin da za a bude kofarsu ga ketare. Takardun fahimtar juna na yin hadin gwiwa bisa shawarar 'ziri daya da hanya daya' da kasar Sin ta kulla tsakaninta da sauran sassan duniya, kamar kasar Italiya, sun tabbatar da ganin kasar Sin ta kara yin hadin gwiwa da sauran sassan duniya, a fannonin samar da kayayyaki da kuma zuba jari. Dokar zuba jari ta baki 'yan kasuwa" wadda kasar Sin ta fitar ta tabbatar da karuwar jarin waje da aka zuba a kasar. A waje daya, yanayin kasuwancin kasar Sin ya samu ingantuwa. A watan Maris, ma'aunin PMI dake nuna halin da masana'antu suke ciki ya kai 50.5%. Wannan adadi ya alamta cewa, yanzu masana'antun kasar Sin na samun farfadowa bayan watanni 3 da suka gabata."

Yuan Da yana ganin cewa, a yayin da tattalin arzikin duniya ke samun karuwa sannu a hankali, tattalin arzikin kasar Sin ma na fuskantar matsin lamba na raguwa, ba abu mai sauki ba ne ga kasar Sin ta samu ci gaban tattalin arzikinta kamar yadda ake fata. Mr. Yuan ya bayyana cewa, "A bana, an hanzarta aiwatar da wasu muhimman manufofi, da kuma wasu muhimman matakai na tsara ci gaban tattalin arzikin kasar. Yanzu wadannan manufofi da matakai sun fara taka rawar a zo a gani. Sakamakon haka, muna cike da imani game da sharudda, da kuma karfin cimma burin neman ci gaban tattalin arziki, da zaman al'umma da ta kafa a farkon shekarar."

Wannan jami'in ya kuma labarta cewa, a farkon rubu'in bana, yawan jarin da gwamnatin kasar ta kebe wa gwamnatocin matakai daban daban na larduna daga baitulmali ya riga ya kai 80% bisa jimillar jarin da za ta kebe musu a duk shekara, ta yadda za a iya tabbatar da samun isassun kudaden samar da wasu kayayyakin more rayuwar al'umma, da kuma taka rawar kasafin kudi wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.

A jiya kuma, kakakin hukumar kula da kudaden musaya ta kasar Sin madam Wang Chunying ta bayyana cewa, yanzu, ana amfani da jari tsakanin kasar Sin da sauran sassan duniya kamar yadda ya kamata, sannan kudaden musaya da aka adana a kasar Sin sun karu kadan.

Bisa alkaluman da aka bayar, an ce, kawo karshen watan Maris, yawan kudaden musaya da aka adana a kasar Sin ya kai dalar Amurka triliyan 3.0988, wato ya karu da dalar Amurka biliyan 26 bisa na karshen shekarar 2018.

Madam Wang Chunying tana mai cewa, "A farkon rubu'in shekarar 2019, darajar kudin Sin RMB ba ta samu tangarda ba, ana amfani da jari tsakanin kasar Sin da sauran sassan duniya kamar yadda ya kamata. An kuma cimma daidaito a kasuwar musayar kudaden duniya."

Madam Wang ta kuma bayyana cewa, a shekarar 2019, hukumarta za ta ci gaba da yin kwazo da himma, wajen inganta yanayin cinikin waje da kuma sassauta sharuddan zuba jari. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China