in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa kan shawarar "ziri daya da hanya daya"
2019-04-27 17:05:59 cri

An gudanar da taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa kan shawarar "ziri daya da hanya daya" karo na biyu a cibiyar taruruka ta tebkin Yanxi dake nan birnin Beijing a yau Asabar, inda shugabannin kasashen duniya 37 da na MDD da asusun IMF suka halarta. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ne ya shugabanci taron tare da gabatar da jawabi mai taken "raya shawarar 'ziri daya da hanya daya' mai kyautatuwa". Xi Jinping yana fatan bangarori daban daban za su yi kokari tare don kara raya shawarar "ziri daya da hanya daya", ta yadda za ta amfanawa jama'ar kasa da kasa.

Game da wannan batu, Xi Jinping ya gabatar da shawarwari uku, na farko, ana fatan bangarori daban daban za su yi kokari tare da kyautata aikin hadin gwiwa don raya shawarar "ziri daya da hanya daya" mai kyautatuwa. Ya ce ya kamata a goyi bayan shigar da ajendar samun ci gaba mai dorewa ta MDD da ake son cimma zuwa shekarar 2030 cikin aikin raya shawarar "ziri daya da hanya daya", da sa kaimi ga bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma da kuma kiyaye muhalli bisa ka'idoji da ma'aunin da kasa da kasa suka amince, ta yadda kasa da kasa za su samu moriya daga cikin aikin da samun ci gaba tare. Na biyu, yana fatan za a tabbatar da ayyukan hadin gwiwa mafi muhimmanci, da kara yin mu'amala da hadin gwiwa a dukkan fannoni. Ya ce ya kamata a sa kaimi ga raya ayyukan more rayuwa, da hadin gwiwar dake tsakanin harkoki, da bunkasuwar tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama'a. Shawara ta uku da ya bayar, ita ce bangarori daban daban za su raya tsarin hadin gwiwa, da kafa dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa a tsakaninsu. Shugaba Xi ya ce ya kamata a sa kaimi ga raya tattalin arzikin duniya mai bude kofa, da kin amincewa da ra'ayin ba da kariya ga cinikayya, da ci gaba da hada shawarar "ziri daya da hanya daya" da manufofin raya kasashe da yankuna, don samun moriyar juna. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China