in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jawabin da shugaban kasar Sin ya gabatar a wurin taron BRF ya samu karbuwa
2019-04-28 16:34:33 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da jawabi yayin bikin bude taron kolin dandalin hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar ziri daya da hanya daya (BRF) karo na biyu da ya gudana a jiya Asabar, jawabin da ya samu karbuwa sosai daga kasa da kasa.

Ana ganin cewa, ra'ayoyin da shugaban ya gabatar a jawabinsa dangane da kulla huldar abota a fannoni daban daban da inganta hadin gwiwar kasa da kasa, za su taimaka ga inganta huldar kasa da kasa a bangarori da dama da kuma cin moriyar juna.

Bernadette Deka-Zulu, darektan zartaswa na cibiyar nazarin manufofi ta kwararrun kasar Zambia ya ce, shawarar ziri daya da hanya daya ta samar da wani sabon dandali na inganta harkokin ciniki da zuba jari a tsakanin kasa da kasa, kuma ta hanyar gina nau'o'in manyan ayyuka, an hade sassan duniya daban daban, matakin da ya samar wa kasashen Afirka damar yin ciniki da kasa da kasa. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China