logo

HAUSA

Babban sakataren kungiyar sadarwa ta kasa da kasa ya taya murnar cimma nasarar harbar na’urar Chang’e-5

2020-11-26 11:10:48 CRI

Babban sakataren kungiyar sadarwa ta kasa da kasa ya taya murnar cimma nasarar harbar na’urar Chang’e-5

Da misalin karfe hudu da rabi na safiyar Talata, aka harba na’urar binciken duniyar wata ta Chang’e-5, kuma wannan ne karon farko da Sin ta dauko samfuran tabo da duwatsu daga wata duniya ta daban. Game da hakan, babban sakataren kungiyar sadarwa ta kasa da kasa (ITU) Zhao Houlin, ya taya Sin murnar cimma wannan nasara ta harbar na’urar Chang’e-5.

Zhao Houlin ya ce, ya taya murnar cimma nasarar harbar na’urar binciken duniyar wata ta Chang’e-5, kuma yana mai fatan na’urar ta Chang’e-5 ta dawo duniya lami lafiya a watan Disamba mai zuwa. Ya ce, rokar Long March-5 ita ma ta gudanar da aikinsa mai kyau, mai kuma matukar faranta rai.

Harbar na’urar Chang’e-5 mataki ne na karshe, bisa matakai 3 na binciken duniyar wata, wato zagayawa, da saukawa, da kuma dawowa, inda za a dauko samfura daga doron duniyar wata. Fasahohin da na’urar za ta yi amfani da su a cikin wannan aiki sun kasance karon farko da Sin take amfani da su a wannan fanni.

Zhao ya ce, aiki mafi muhimmanci shi ne dawowarta duniyarmu. Idan an iya daidaita batutuwa masu ruwa da tsakai duka don gane da dawowar na’urar, za a yi imani da cewa, ba shakka ‘yan sama jannati za su taka kasan duniyar wata nan gaba ba da jimawa ba.

Na’urar binciken duniyar wata ta Chang’e-5 za ta yi amfani da matakai biyu wajen dauko samfuran tabo da duwatsu daga doron duniyar wata, wato daukowa daga fuska, da hakar kasa mai zurfi. Dangane da lamarin, Zhao Houlin ya ce, a karon farko Bil Adama sun haka duniyar wata, matakin da ya baiwa masu kimiyya damar binciken sinadaran hada duniyar wata, da yadda duniyar wata ta hadu a halin yanzu. Matakin da zai samar da tubali na bincike da yin amfani da duniyar wata a nan gaba.

Ban da wannan kuma, Zhao ya yi maraba da kokarin da Sin take yi, na kara hadin kanta da sauran kasashe a fannin zirga-zirgar sararin samaniya. A matsayin wata hukuma dake kula da fasahar bayanai da aikin sadarwa a MDD, kungiyarsa ta ITU za ta kara hadin kai da kasar Sin a fannoni masu ruwa da tsaki. Zhao ya jaddada cewa, aikin sadarwa ta wayar iska, kimiyya ce mai tushe ga binciken sararin samaniya. Ya ce, Sin tana yin hadin kai yadda ya kamata da kasashen duniya ta fuskar sararin samaniya. Ban da injiniyoyi da fasahohin wutar lantarki, fasahar daidaita fadin inda sakon iska, ko sauti ke iya isa na da muhimmanci matuka.

Don haka ya ce kungiyarsa na gudanar da aikin yin amfani, da kuma kiyaye fadin inda sakon iska ko sauti ke iya isa, tana kuma sulhuntawa tsakanin kasashen daban-daban kan wannan batu. Daga nan sai ya yi fatan Sin za ta kara hadin kanta da sauran kasashe a wannan fanni, ta yadda za a ingiza bunkasuwar aikin binciken sararin samaniya. (Amina Xu)