logo

HAUSA

Wadanne bayanan aka gano daga jawabin Xi yayin bikin baje kolin Sin da ASEAN?

2020-11-28 16:49:34 CRI

Da safiyar jiya Jumma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo yayin bikin baje koli na Sin da ASEAN karo na 17 da bikin kaddamar da taron kolin kasuwanci da zuba jari na Sin da ASEAN. Ya sake halartar babban bikin baje kolin kasa da kasa bayan ya halarci bikin baje kolin hada-hadar ba da hidimomi da aka shirya a birnin Beijing da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin daga ketare da aka shirya a birnin Shanghai.

Sakamakon tasirin annobar cutar numfashi ta COVID-19, an jinkirta lokacin shirya bikin baje koli na Sin da ASEAN daga watan Satumba zuwa ranar 27 zuwa 30 ga watan Nuwamba, duk da cewa, ana ci gaba da fama da yaduwar annobar, an dauki sabon salo wajen shirya bikin, inda har ya kai matsayin koli a tarihi.

Wadanne bayanan aka gano daga jawabin Xi yayin bikin baje kolin Sin da ASEAN?

Dalilin da ya sa aka ce bikin ya kai matsayin koli shi ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi a yayin bikin, kana firayin ministan Laos da firayin ministan Kambodia da shugaban Indonesia da shugaban Myama da shugaban Philipines da sauran shugabannin kasashe mambobin kungiyar ASEAN, su ma sun gabatar da jawabai ta kafar bidiyo.

Wadanne bayanan aka gano daga jawabin Xi yayin bikin baje kolin Sin da ASEAN?

Kana dalilin da ya sa aka ce an dauki sabon salo wajen shirya bikin shi ne, a karo na farko an shirya bikin ta hanyoyi biyu, wato ta kafar bidiyo tare kuma da gaba da gaba, wato an shirya bikin a babban daki mai fadin muraba’in mita dubu 104, inda aka kebe wuraren nune-nune da yawansu ya kai 5400, a sa’i daya kuma, kamfanoni sama da 1500 sun halarci bikin ta kafar bidiyo, irin wannan sabon salon da aka yi amfani da shi ya sa kaimi kan sayayya, saboda babu kayyaden lokaci da wuri.

Babban taken bikin baje kolin na Sin da ASEAN na wannan karo shi ne “Gina shawarar ziri daya da hanya daya tare domin farfado da tattalin arzikin zamani tare”.

A cikin jawabin da ya yi jiya, shugaba Xi ya gabatar da shawarwari guda hudu, wato kara karfafa aminci da juna domin tsara tsarin raya kasashen yankin, da kara hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin sassan biyu domin hanzarta farfadowar tattalin arziki daga dukkan fannoni a yankin, da kara sa kaimi kan kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha domin zurfafa hadin gwiwar tattalin arzikin zamani dake tsakanin sassan biyu, da kara mai da hankali kan hadin gwiwa wajen kandagarkin annobar COVID-19 domin kara karfin kiwon lafiyar jama’a a yankin.

Abu mai muhimmanci yayin da ake tsara tsarin raya kasashen yankin gabashin Asiya shi ne, gudanar da hadin gwiwa bisa shawarar ziri daya da hanya daya da kuma babban shirin cudanyar juna tsakanin kasashen ASEAN.

A bana aka kaddamar da hadin gwiwar tattalin arzikin zamani dake tsakanin kasar Sin da ASEAN, kuma a cikin jawabinsa, shugaba Xi ya bayyana cewa, kasarsa tana son hada kai da kasashe mambobin ASEAN domin ingiza habakar tattalin arzikin zamani tsakaninsu, ta hanyar amfani da damammakin sabon zagayen juyin juya halin kimiyya da fasaha da sauye-sauyen sana’o’i.

Shugaba Xi ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bude kofa ga ketare, tare kuma da kara karfafa cudanyar tattalin arziki a cikin gida da kuma tsakanin kasa da kasa, ta yadda za ta ba da gudummuwa kan farfadowar tattalin arzikin duniya. A cewarsa, ta haka daukacin kasashen duniya, ciki har da kasashen ASEAN za su samu moriya daga ci gaban kasar Sin. Ana cike da imanin cewa, makomar hadin gwiwar tsakanin Sin da ASEAN tana da haske.(Jamila)