logo

HAUSA

Masanan kasashen yamma na sanya kokonta a zukatan al’umma ta hanyar kiran hukumomin al’umma da cibiyoyin tsare mutane a Xinjiang

2020-11-28 17:36:39 CRI

Gwamnatin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin, ta bayyana furucin da wasu masana na kasashen yamma ke yi kan hukumomin kula da al’umma na jihar, a matsayin wani yunkuri na sanya rudani ko kokonto a zukatan jama’a.

Kakakin ofishin yada labarai na gwamnatin jihar ne ya bayyana haka, yayin wani taron manema labarai, inda wani ma’akacin gidan talabijin na CNN ya yi tambaya game da ikirarin wasu masanan kasashen yamma dake amfani da hotunan tauraron dan Adam domin nazartar jihar Xinjiang, inda kuma suka bayyana hukumomin kula da al’umma na jihar a matsayin cibiyoyin tsare mutane.

Kakakin ya bayyana cewa, cikin rahotonta, wata cibiyar bincike ta kasar Australia, ta bayyana dukkan gine-ginen da aka katange a Xinjiang a matsayin cibiyoyin tsare jama’a, bayan kuma hukumomi ne dake hidimtawa al’umma. A kara da cewa, cibiyar tsare mutane a Turpan da rahoton ya yi ikirari, ginin ofisoshin gwamnati ne, na kashgar kuwa, gidan raino ne da wajen adana kayayyaki da kuma makaranta da sauransu.

Ya ce wasu masu bincike dake zaman kansu kamar cibiyar ta Australia, ba cibiyoyin binciken ilimi ba ne, wurare ne da aka kafa domin adawa da Sin, wadanda Amurka ke jan ragamarsu.

Ya ce Xinjiang a bude take, don haka babu bukatar amfani da hotunan tauraron dan Adam domin nazartarta. Ya ce suna maraba da bakin da suke da sahihiyar manufa, su ziyarci jihar domin kara fahimtarta. (Fa’iza Mustapha)