logo

HAUSA

An kaddamar da cibiyar horo ta Luban ta kasar Sin a Nigeria

2020-11-28 16:30:45 CRI

An kaddamar da cibiyar horo ta Luban ta kasar Sin a Nijeriya, da nufin ba da horon dabarun fasaha domin taimakawa daliban kwaleji cimma bukatun kasuwa.

Cibiyar wadda jami’ar Abuja ta karbi bakuncinta, za ta fara ne a matakin farko da kwasakwasan da suka hada da kula da zirga-zirgar jiragen kasa da gadoji da ramukan jiragen kasa.

Da yake jawabi yayin bude cibiyar Luban, mataimakin shugaban jami’ar Abuja, Abdulrasheed Na’Allah, ya ce cibiyar da aka kafa da tallafin jami’ar kimiyya ta Sin da Jamus dake Tianjin da kwalejin fasaha da nazarin sufurin jiragen kasa ta Tianjin, za ta taimaka wajen inganta kwarewar matasa yayin da ake inganta shawarar ziri daya da hanya daya ta gwamnatin kasar Sin.

A cewarsa, daga cikin manufofin kafa cibiyar akwai musaya tsakanin al’ummun bangarorin biyu tun daga tushe, wadda za ta iya karfafa abota tsakanin ‘yan Nijeriya da Sinawa har abada, haka kuma misali ne na sahihiyar hulda tsakanin kasashen dake son kulla abota ta kwarai. (Fa’iza Mustapha)