logo

HAUSA

Cikin kwanaki 20 a jere, adadin masu kamuwa da cutar COVID-19 a Amurka ya kai sama da dubu 100 kowace rana

2020-11-29 17:00:23 CRI

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasar Amurka ta sanar a jiya Asabar cewa, bisa rahoton da ta samu a ranar 17 ga wata, adadin karuwar masu kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a duk fadin Amurka a wannan rana ya kai sama da dubu 176, lamarin da ya nuna cewa, cikin kwanaki 20 a jere, adadin masu kamu da cutar COVID-19 a kasar ya kai sama da dubu 100 kowace rana.

Bisa kididdigar da jami’ar Johns Hopkins ta kasar Amurka ta yi, daga ranar 9 ga watan Nuwamba zuwa 27 ga wata, adadin karuwar masu kamuwa da cutar numfashi ta COVID-19 ya kai sama da miliyan 1 cikin kwanaki 6. Kana, ya zuwa daren ranar 28 ga wata, agogon gabashin kasar Amurka, gaba daya, adadin masu kamuwa da cutar a kasar Amurka ya kai sama da miliyan 13.23, yayin da mutane sama da dubu 266 suka rasa rayukansu sakamakon cutar, adadin yana kan gaba cikin dukkanin fadin duniya.

Masanin cibiyar nazarin Scripps ta kasar Amurka Eric Topol ya ce, ba kawai ana fama da matsalar karancin gadaje a asibitoci ba ne, har ma, babu isassun likitoci da nas-nas. Idan kasar Amurka ta fidda manufofin dakile yaduwar cutar dake shafar yawon shakatawa a lokacin hutun bikin nuna fatan alheri na Thanksgiving, da tilastawa al’umma sanya abin rufe hanci da baki, da kuma farfado da tattalin arziki da sauransu, hakan zai fi kyau a maimakon daukar matakan siyasantar da batun, yanayin da ake ciki a halin yanzu zai bambanta kwarai da gaske.

Yanzu, ana cikin hutun bikin Thanksgiving a kasar Amurka, cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasar ta yi kira ga al’ummomin kasar da su zauna a gida yayin bikin, domin rage barazanar kamuwa da cutar, da kuma hana yaduwar annobar. (Maryam)