logo

HAUSA

Kamata ya yi a yi rigakafin ciwon sukari ta hanyar sauya salon zaman rayuwa

2020-11-29 18:45:26 CRI

Ranar 14 ga watan Nuwamba na ko wace shekara, ranar ce ta ciwon sukari da MDD ta ware. Ciwon sukari, wani nau’in ciwo ne da ke shafar yanayin sarrafa sinadaran jiki, kuma mutane da yawa suna fama da shi a duk duniya. Kasar Sin tana samun saurin karuwar yawan masu kamuwa da ciwon. Yanzu mutane fiye da miliyan 110 suna fama da ciwon na sukari a kasar Sin baki daya, yayin da wasu miliyan 150 suke dab da kamuwa da ciwon. Cututtukan da mutane su kan kamu da su sakamakon ciwon sukari su kan illanta lafiyar jijjiyoyin jini, idanu, koda, kafafu da sauran sassan jikin dan Adam, suna kuma sanya mutane da yawa su nakasa ko rasa rayuka. Likitoci sun ba da shawarar yin rigakafin ciwon sukari ta hanyar sauya salon zaman rayuwa.   Wasu likitoci masu ilmin cututtukan da suka shafi yanayin sarrafa sinadaran jiki na kasar Sin sun yi bayani da cewa, ya zuwa yanzu ba a san yadda ake kamuwa da ciwon na sukari kwata kwata ba tukuna. Yadda aka gaji ciwon daga mahaifa, yanayin muhalli, salon zaman rayuwa, yawan ayyuka da dai sauransu sun haifar da yadda jikin dan Adam ba ya samar da isasshen sinadarin Insulin da kuma yadda sinadarin Insulin ba ya aiki yadda ya kamata, a karshe sai a kamu da ciwon sukari. Ciwon sukari mai nau’in 2, ciwon sukari ne da a kan kamu da shi a kasar Sin. Matsalar kiba ta kan sa mutane su kamu da ciwon sukari mai nau’in 2.

Sakamakon bunkasuwar birane a kasar Sin, ya haddasa kyautatuwar zaman rayuwa da kuma raguwar motsa jiki a kasar Sin, ta yadda aka samu saurin karuwar masu fama da ciwon sukari a kasar. Hakika dai ana iya yin rigakafin ciwon sukari, musamman sauya salon zaman rayuwa yana rage yawan masu kamuwa da ciwon. Cin abinci ta hanyar da ta dace, motsa jiki a kai a kai da kuma rage nauyin jiki suna kare mutane daga kamuwa da ciwon sukari.

Madam Zhang Chuji, wata likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana bayani da cewa, mutane suna fuskantar barazanar kamuwa da ciwon sukari ne sakamakon matsalar kiba, ko hawan jiki, ko karuwar man da ke cikin jini, ko gadon ciwon sukari daga mahaifa da kakani, ko fama da matsalar karuwar sukari cikin jini lokacin samun ciki, ko kuma haihuwar jariran da nauyinsu ya wuce kilo 4. Kamata ya yi a dauki matakan yin rigakafi.

Madam Zhang ta ba da shawarar cewa, mutane ‘yan sama da shekaru 40 a duniya musamman ma wadanda mahaifansu ko kakanninsu suka yi fama da ciwon sukari kamata ya yi su mai da hankali kan binciken lafiya da kuma sauya salon zaman rayuwa. Ban da haka kuma, dole ne a je ganin likita don tabbatar da ko an kamu da ciwon ko a’a tun da wuri, sa’an nan a sha magani tun da wuri.

Yanzu haka sauya salon zaman rayuwa, hanya ce mafi dacewa kuma mafi tsimin kudi wajen kare mutane daga kamuwa da ciwon sukari. Ma’anar sauya salon zaman rayuwa a taikaice ita ce cin abinci ta hanyar kimiyya da kara motsa jiki. Yawancin masu fama da ciwon sukari su kan ci abinci mai maiko da yawa, ko cin abubuwa fiye da yadda suke bukata. Don haka wajibi ne a rage cin abinci mai maiko da yawa, tare kuma da motsa jiki a kai a kai da kuma rage nauyin jiki. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan