logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya yi Allah wadai da harin shiyyar arewa maso gabashin kasar

2020-11-29 15:27:47 CRI

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da harin da aka kaddamar kan manoma a yankin jahar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar, wanda aka bada rahoton kashe gomman mutane.

A sanarwar da hukumomin kasar suka fitar bayan faruwar lamarin a safiyar ranar Asabar, shugaba Buhari ya ce, ya yi Allah wadai da kashe hazikan manoma wadanda ’yan ta’adda suka kashe a jahar Borno. A cewar shugaban dukkan jama’ar kasar baki daya suna alhinin wannan kisa na rashin hankali.

Wasu da suka shaida faruwar lamarin sun ce, an kaddamar da harin ne a lokacin da wasu manoma suke girbin amfanin gonarsu inda maharan wadanda ake kyautata zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne suka afka musu ta hanyar yaudara da zummar gabatar musu da bukatar neman abinci.

Sai dai kuma, sanarwar ba ta bayar da hakikanin yawan mutanen da lamarin ya rutsa da su ba, amma an tabbatar cewa an kai harin ne inda aka kashe manoman shinkafa a gonakinsu dake garin Zabarmari, a karamar hukumar Jere dake jahar Borno. (Ahmad)