logo

HAUSA

Mutane fiye da miliyan 9 da dubu 980 a jihar Xinjiang suna amfani da mitar wutar lantarki ta zamani

2020-11-30 16:11:08 CRI

Bisa kididdigar da kamfanin samar da wutar lantarki da yanar gizo na kasar Sin dake jihar Xinjiang ya yi, ya zuwa yanzu, mutane miliyan 9 da dubu 981 da dari 6 suna amfani da mitar wutar lantarki ta zamani. Kana kamfanonin samar da wutar lantarki da yanar gizo sun samar da fasahohin nazari na zamani don gudanar da ayyukan gyara matsalolin wutar lantarki, da sayen wutar lantarki da sauransu.

Shugaban sashen fasahohin yanar gizo na cibiyar bada hidima ta kamfanin samar da wutar lantarki da yanar gizo na kasar Sin dake jihar Xinjiang Zhang Jianwen ya bayyana cewa, wadannan mutanen jihar suna amfani da mitar wutar lantarki ta zamani, abun da ya alamta cewa, sun samu damar sayen wutar lantarki a cikin gida, ta hakan kuma, za a rage kuskuren da ake samu yayin da ma’aikatan kamfanin suke aikin kidaya yawan wutar lantarki da aka yi amfani da shi gidaje daya bayan daya. (Zainab)