logo

HAUSA

Wajibi ne gwamnatin Australiya ta nemi gafara daga wajen al'ummar Afghanistan

2020-11-30 21:04:04 CRI

Firaministan kasar Australiya Scott Morrison ya bukaci kasar Sin ta nemi gafara daga wajen kasarsa, saboda wani hoto da kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya wallafa a shafinsa na Twitter dangane da yadda wani sojan Australiya ya kashe yaran kasar Afghanistan.

Dangane da lamarin, madam Hua Chunying kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana yau Litinin a nan Beijing cewa, wajibi ne gwamnatin Australiya ta yi tunani sosai kan abun da sojojinta suka aikata a Afghanistan ta kuma gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban kotu, kana ta nemi gafara daga wajen al’ummar Afghanistan, sa’an nan ta yi wa kasashen duniya alkawarin ba za ta sake aikata irin wannan ta’asa mai ban tsoro a nan gaba ba. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan