logo

HAUSA

Yawan kayayyakin da aka yi jigilarsu a kasar Sin a bana ya zarce biliyan 70

2020-11-30 14:47:59 CRI

Bisa kididdigar da hukumar kula da aikin aika wasika da kaya ta kasar Sin ta yi, ya zuwa ranar 16 ga wannan wata, yawan kayayyakin da aka yi jigilarsu a kasar Sin ya zarce biliyan 70, wanda ya fi na shekarar bara. An samu babban ci gaba a fannin aika kayayyaki a kasar ne sakamakon bunkasuwar ciniki ta yanar gizo.

A bana, aka kammala tsara hidimar bibiyar kayayyaki ta yanar gizo a kasar Sin, wato bisa wannan tsari, kowane kaya yana da takardar dake nuna inda ya fito, sannan ana iya neman shi da sanin inda yake a duk hanyar da aka yi jigilarsa. (Zainab)