logo

HAUSA

Kamfanin gine gine na kasar Sin zai taimaka wajen bunkasa fannin sufurin Namibia

2020-12-01 09:45:08 CRI

Shirin da gwamnatin kasar Namibia ta yi na yunkurin mayar da kasar wata babbar cibiyar sufurin kudancin Afrika zai tabbata ne ta hanyar ayyukan yin kwaskwarima da daga matsayin hanyar layin dogon kasar tsakanin yankin Walvis Bay da Arandis.

Aikin wanda kamfanin gine gine na kasar Sin CGGC dake Namibia zai gudanar, ana sa ran aikin zai bunkasa shirin hade layukan dogo na kasar da kashi 70 bisa 100, kuma zai bunkasa fannin harkokin sufurin jiragen kasa na kungiyar kasashen raya ci gaban shiyyar kudancin Afrika SADC.

Ministan ayyuka da sufuri na kasar Namibia, John Mutorwa, wanda ya gabatar da jawabi a bikin kaddamar da aikin, ya ce aikin wanda za a gudanar a shiyyar tekun yammacin Namibia zai hade yankin mai nisan kilomita 107.5.

Gwamnatin kasar Namibia zata samar da kashi 56 bisa 100 na kudaden aiki yayin da bankin raya cigaban Afrika zai samar da rancen kashi 44 bisa 100 na kudaden aikin.(Ahmad)