logo

HAUSA

Yawan mutanen da suka kamu da COVID-19 a Afrika ya zarce miliyan 2.16

2020-12-01 09:57:09 CRI

Yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a nahiyar Afrika ya kai 2,163,284 ya zuwa yammacin Litinin, kamar yadda hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika CDC ta sanar.

Hukumar dakile cutuka ta nahiyar ta bayyana cikin sanarwar cewa, yawan mutanen da cutar ta hallaka a nahiyar ya kai 51,708.

Jimillar mutanen da suka warke daga cutar ta COVID-19 a fadin nahiyar Afrika ya kai 1,831,435 ya zuwa yanzu, a cewar Afrika CDC.

Kasashen Afrika da annobar COVID-19 ta fi shafa ta fuskar yawan masu kamuwa da cutar sun hada da Afrika ta kudu, Morocco, Masar, da Habasha, a bisa alkaluman da Afrika CDC suka nuna.

Shiyyar kudancin Afrika ne cutar COVID-19 ta fi yiwa illa ta fuskar yawan mutanen da suka kamu da cutar da wadanda cutar ta kashe.(Ahmad)