logo

HAUSA

Mataimakin shugaban Zimbabwe yayi murabus

2021-03-02 09:57:41 CRI

Daya daga cikin mataimakan shugaban kasar Zimbabwe biyu, Kembo Mohadi, yayi murabus daga kan mukaminsa a wani sakon da ya wallafa a ranar Litinin bayan wani zargi da aka yada a kafafen yada labarai inda ake zarginsa da neman yin mu’amala da wata matar aure.

A kwanan nan ne aka yada wasu muryoyi uku a shafukan intanet wadanda ke alakanta Mohadi da zargin neman yin lalata da wasu mata, amma mista Mohadi ya musanta zargin da ake masa, yana mai cewa abokan hamayyar siyasarsa ne suke masa bita-da-kulli.

A wata sanarwar da ya fitar da yammacin ranar Litinin, Mohadi, mai shekaru 71 a duniya, ya ce ya yanke shawarar sauka daga mukaminsa ne domin kiyaye martabar gwamnatin kasar.(Ahmad)