logo

HAUSA

Kasar Sin ta ki yarda da yadda kasar Amurka ta tsoma baki cikin harkokin gidanta

2021-03-02 21:45:12 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Wang Wenbin ya furta a yau Talata cewa, kasar Sin ta ki yarda da yadda kasar Amurka ta fake da batun hakkin dan Adam, wajen neman shafawa manufar kasar Sin ta kula da yankin Xinjiang bakin fenti, da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar.

An ce, a kwanan nan, shugabar majalisar wakilai ta kasar Amurka, Nancy Pelosi, ta gana da wasu ’yan Uygur “masu kare hakkin kabila” na wai, wadanda a hakika mutanen dake neman balle yankin Xinjiang daga kasar Sin. (Bello Wang)

Bello