logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kira ga kasashen duniya su kara tallafawa Yemen

2021-03-02 10:45:22 CRI

Mataimakin zaunannen wakilin Sin a MDD Dai Bing, ya bukaci kasashen duniya, su kara tallafawa Yemen, domin kare aukuwar yunwa a kasar.

A cewar Dai Bing, Yemen na fama da tarin kalubale da suka hada da rikici da na tattalin arziki da COVID-19 da rashin wadatar abinci, wadanda suka jefa ta cikin matsananciyar matsalar jin kai. Ya ce, ya zama wajibi kasashen duniya su gaggauta daukar mataki, da kara taimakawa Yemen da kare ta’azzarar matsalar jin kai da kokarin kaucewa karuwar yunwa a kasar.

Ya kara da cewa, ya kamata hukumomin MDD su gudanar da ingantattun ayyukan jin kai da karfafa hada hannu da kasashen yankin da hukumomi. Ya ce dole ne dukkan bangarorin dake rikici su tabbatar da ayyukan jin kai sun gudana ba tare da wani tsaiko ba, sannan kayayyakin jin kai sun isa ga mutane masu bukata, tare kuma da tabbatar da bada kariya ga masu rauni kamar mata da yara.

Bugu da kari, Dai Bing, ya ce kasar Sin za ta ci gaba da samar da abinci da magunguna da sauran agajin jin kai ga Yemen. Kana Sin za ta hada hannu da kasashen duniya, tare da kokarin bada gudunmuwa wajen saukaka walhalun jin kai da dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Yemen, nan bada dadewa ba. (Fa’iza Mustapha)