logo

HAUSA

Kasashe daban daban sun nuna goyon baya ga kasar Sin a taron kare hakkin bil Adama

2021-03-02 19:32:23 CRI

A kwanan nan, kasashe daban daban sun bayyana ra’ayinsu na nuna goyon baya ga kasar Sin, a wajen zama na 46 na kwamitin kare hakkin dan Adama na MDD.

Kasar Sudan ta Kudu ta jinjinawa hukumar yankin Xinjiang na kasar Sin, kan yadda ta mai da rayuka, da lafiyar jama’a a gaban komai. A nata bangare, kasar Burundi ta yabi yadda kasar Sin take kokarin ba da taimako ga sauran kasashe, a kokarinsu na dakile cutar COVID-19. Ta kuma jinjina kasar Sin kan nasarorin da ta samu, a fannonin tinkarar ’yan ta’adda a yankin Xinjiang na kasar, da kokarin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma.

A nata bangare kuwa, kasar Chadi ta ce yadda gwamnatin kasar Sin take aiwatar da manufar “Kasa daya, tsarin mulki biyu” a yankin Hong Kong na kasar abun yabawa ne. (Bello Wang)

Bello