logo

HAUSA

Sanarwar kididdigar ci gaban tattalin arziki da zaman al’umma na shekarar 2020 ta shaida nasarorin da al’ummar Sinawa suka cimma

2021-03-02 14:03:58 CRI

A ranar Lahadi da ta gabata ne, hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar da sanarwar kididdigar ci gaban tattalin arziki da zaman al’umma na kasar Sin na shekarar 2020, sanarwar da ta shaida manyan nasarorin da al’ummar Sinawa suka cimma bisa kokarinsu a shekarar da ta gabata.

Sanarwar kididdigar ci gaban tattalin arziki da zaman al’umma na shekarar 2020 ta shaida nasarorin da al’ummar Sinawa suka cimma_fororder_微信圖片_20210302135713

Sanarwar ta yi nuni da cewa, a shekarar 2020, ma’aunin tattalin arziki, wato GDP na kasar Sin ya kai kudin Sin yuan triliyan 101 da biliyan 598.6, adadin da ya karu da kaso 2.3% bisa na shekarar 2019, lamarin da ya sa ta zama kasa daya kacal a duniya da ta samu karuwar tattalin arzikinta. Baya ga haka, yawan tattalin arzikin kasar Sin ya dau sama da kaso 17% na tattalin arzikin duniya baki daya, hakan ya sa ta zama babban inji dake ingiza farfadowar tattalin arzikin duniya. A game da wannan, Diego Mazzoccone, shugaban zartaswa na cibiyar nazarin harkokin siyasa da tattalin arziki na kasar Sin ta kasar Argentina ya bayyana cewa,“Kasar Sin ta kasance inji ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya, duba da cewa, bunkasuwar kasar Sin tuni ta zama muhimmin karfin da ke sa kaimin bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Duk da cewa annobar Covid-19 ta haifar da mummunan tasiri ga tattalin arzikin kasar, amma kasar ta dauki matakai cikin sauri, kamfanoninta ma sun gaggauta farfado da ayyukansu, baya ga yadda bangarorin al’ummar kasar suka nuna cikakken goyon baya ga matakan da gwamnati ta dauka na farfado da tattalin arziki. Ko da yake tattalin arzikin kasar ma ya ragu a sakamakon barkewar annobar, amma ya farfado cikin sauri, har ya sa kaimi ga farfadowar tattalin arzikin duniya.”

Sanarwar kididdigar ci gaban tattalin arziki da zaman al’umma na shekarar 2020 ta shaida nasarorin da al’ummar Sinawa suka cimma_fororder_微信圖片_20210302135702

Sanarwar ta kara da cewa, a shekarar 2020, kasar ta samu nasarorin a zo a gani a kokarinta na yaki da talauci. Bisa ma’aunin da ake aiwatarwa yanzu, a shekarar 2020, an fitar da dukkanin al’umma masu fama da talauci kimanin miliyan 5 da dubu 510 da suka fito daga karkarar kasar, baya ga masu fama da talauci da aka yi musu rajista a larduna 22 da ke tsakiya da yammacin kasar, wadanda aka tabbatar cewa, sun samu abinci da sutura da ilmi da kiwon lafiya da gidajen kwana da ruwan sha mai inganci. A game da wannan, shugaban cibiyar nazarin harkokin gabas mai nisa karkashin kwalejin nazarin kimiyya na kasar Rasha, Alexey Maslov ya bayyana cewa,“Babu shakka, wannan gaggarumar nasara ce ga kasar Sin, da ma duniya baki daya. A karon farko a tarihin dan Adam, jama’a masu yawa irin haka sun fita daga kangin talauci a lokaci guda. Fasahohi da dabaru da kasar Sin ta aiwatar wajen saukaka fatara sun cancanci kasashen Afirka, da na Latin Amurka, da dai sauransu su yi nazari, kuma su yi koyi da su.”

Sanarwar kididdigar ci gaban tattalin arziki da zaman al’umma na shekarar 2020 ta shaida nasarorin da al’ummar Sinawa suka cimma_fororder_微信圖片_20210302135654

Sanarwar ta kuma nuna cewa, a sakamakon yadda kasar Sin ta shawo kan annobar tare da sa kaimin farfadowar kamfanoni da sauri, ‘yan kasuwa na ketare sun gaggauta zuba jari a kasar Sin, har ma a shekarar 2020 da ta gabata, yawan jarin waje da kasar Sin ta yi amfani da su, ya kai kimanin yuan triliyan guda, adadin da ya karu da kaso 6.2% bisa na bara. A game da wannan, Zhan Xiaoning, shugaban sashen kula da harkokin zuba jari da kamfanoni na taron MDD dangane da harkokin zuba jari da ci gaba(UNCTAD)ya bayyana cewa, “Yadda tattalin arzikin kasar Sin ya farfado da sauri, ya jawo hankalin ‘yan kasuwar ketare. A yayin da ake fuskantar annobar, yadda kamfanoni na kasa da kasa suke dogara ga tsarin samar da kayayyaki na kasar Sin ya sa ci gaba da zuba jari a kasar. Baya ga haka, yadda kasar Sin ta kara bude wasu sana’o’inta ma ya sa kaimi ga ‘yan kasuwa su zuba jari a ciki. Matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka na saukaka harkokin zuba jari sun taimaka ga kiyaye jarin da ‘yan kasuwar ketare ke zubawa a kasar.” (Lubabatu)