logo

HAUSA

Guterres bai ji dadin sakamakon taron taimakawa kasar Yemen ba

2021-03-02 10:41:29 CRI

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana cewa, bai ji dadin sakamakon taron manyan jami’ai game da alkawarin da aka yi na taimakawa kasar Yemen ba.

Wata sanarwa da babban jami’in na MDD ya fitar, ta nuna cewa, jami’an sun yi alkawarin taimakawa kasar ce da kimanin dala biliyan 1.7, kasa da alkawarin da aka yi a shekarar da ta gabata, kana kasa da dala biliyan 1 kan alkawarin da aka yi, a taron da ya gudana a shekarar 2019.

Sanarwar ta kara da cewa, MDD za ta ci gaba da goyon bayan al’ummar Yemen dake fama da yunwa. Yana mai cewa, hanya daya tilo ta tabbatar da zaman lafiya a kasar, ita ce hanzarta tsagaida bude wuta a fadin kasar, da kafa matakan yarda da juna, da damawa da kowa, da shirya zabe karkashin kulawar MDD, tare da goyon bayan kasasheh duniya.

A jawabinsa yayin taron dai, Guterres ya nemi dala biliyan 3.85 ne, don gudanar da ayyukan jin kai a kasar ta Yemen a shekarar 2021.

A nasa jawabin, darektan shirin samar da abinci na duniya, David Beasley, ya bayyana cewa, ana bukatar dala biliyan 1.9 domin magance matsalar yunwa a Yemen, baya ga wasu karin kudaden don gudanar da wasu ayyukan jin kai.(Ibrahim)