logo

HAUSA

WHO:Kasashen Afirka sun fara cin gajiyar alluran riga kafi karkashin shirin COVAX

2021-03-02 10:32:58 CRI

A makon jiya ne kasashen Ghana da Cote d’Ivoire, suka karbi kason farko na alluran riga kafin COVID-19 karkashin shirin nan na COVAX.

Wata sanarwa da hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta fitar ta bayyana cewa, karkashin shirin na COVAX, kasar ta karbi allurai 600,000 a ranar 24 ga watan Fabrairun da ya gabata, bayan kwanaki biyu kuma kasar Cote d’Ivoire ta karbi nata kason na allurai 504,000. Sanarwar ta ce, rabon alluran, wata manuniya ce dake nuna girma da sarkakiyar shirin raba alluran riga kafi a tarihi. Baki daya, shirin na COVAX, yana fatan raba a kalla alluran riga kafi biliyan biyu nan da karshen shekarar 2021, ciki har da allurai a kalla biliyan 1.3 ga kasashe 92, domin taimaka musu, karkashin shirin da hukumar WHO ke jagoranta.

A jawabinsa, babban darektan hukumar lafiya ta duniya (WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana cewa, “wannan rana ce da galibinmu ke mafarkin zuwanta, inda muka kwashe sama da watanni 12 muna aiki” Amma a cewarsa, nasara na nan tafe. Wannan somin tabi ne, dangane da manufar kafa shirin na COVAX”. (Ibrahim)