logo

HAUSA

Amurka ta kakabawa wasu hukumomi da ‘yan kasar Rasha takunkumi kan sanyawa Navalny guba

2021-03-03 11:19:00 CRI

A jiya ne, kasar Amurka ta sanar da kakaba takunkumi kan wasu hukumomin Rasha da wasu ‘yan kasar, bisa zarginsu da hannu wajen sanyawa mai adawa da fadar Kremlin Alexei Navalny guba.

Da yake yiwa manema labarai karin haske kan lamarin, wani babban jami’a a gwamnatin kasar Amurka ya bayyana cewa, hukumomin leken asirin Amurka sun gano cewa, hukumar leken asirin tarayyar Rasha, ta sanyawa Navalny gubar nan ta Vovichok ce, a ranar 20 ga watan Agustan shekarar 2020.

Jami’in ya kara da cewa, wannan shi ne mataki na farko da Amurka ta dauka kan wannan batu, kuma wasu kari na nan tafe. Yana mai cewa, Amurka za ta yi aiki tare da kawayenta na Turai, wajen yin kira da a tunkari Rasha.

A halin da ake ciki kuma, ma’aikatar harkokin wajen Rasha, ta bukaci gwamnatin Amurka, “da ta guji wasa da wuta”.  Wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar a shafinta na Intanet, ta yi kira takunkumin na Amurka “ a matsayin takala kan Rasha” ta hanyar da ba ta dace ba.

Ta ce Rasha, za ta mayar da martani ta hanyar da ta dace, za kuma ta ci gaba da kare muradunta.(Ibrahim)